Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

  • Wata bishiya mai yawan shekaru ta fadi, inda ta fado kan wasu mutane da ke karkashin ta suka mutu
  • Rahotanni sun bayyana cewa, bishiyar ta kai shekaru 100 a yankin, lamarin kuma ya girgiza mutane
  • Wani mutum ya jikkata, wanda tuni aka dauke shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa

Oyo - Mutane hudu ne ake fargabar sun mutu yayin da wani kuma ya samu munanan raunuka a lokacin da wata tsohuwar bishiyar '' Odan'' ta fadi sakamakon guguwa mai karfi a yankin Saabo da ke cikin garin Oyo a ranar Litinin, Premium Times ta ruwaito.

Tsohuwar bishiyar ta ba da mafaka ga mahauta, kananan motoci da matuka baburan kasuwanci tare da rassanta da suka yadu a mashahurin kasuwar kayan abinci a cikin garin Oyo.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Akeebu Alarape, Shugaban Kasuwar Saabo ta garin Oyo, ya shaida wa NAN cewa bishiyar ta kai kimanin shekaru 100.

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa
Taswirar jihar Oyo | Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter

Mista Alarape ya ce wasu masu aikin yankan bishiya hudu da aka gayyata don sare bishiyar ba su yi nasara ba har sai da na biyar ya zo tukuna ya sami damar yanke wasu sassansa don fara aikin ceto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata 'yar kasuwa mazauna yankin, Kareemot Ejide, 'yar shekara 65, ta ce ta san bishiyar tun tana yarinya.

A cewar Akeem Ojo, shugaban hukumar tsaron yankin Yarbawa ta "Amotekun" a yankin Ci gaban Karamar Hukumar Atiba, bishiyar ta fadi ne da misalin karfe 6 na yamma.

A cewar Ojo:

“Wata daliba mace a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Special), Oyo, wata mata da jariri daure a bayanta da wani yaro da take rike da shi an ciro su daga gindin bishiyar.

Kara karanta wannan

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

“Mutum daya ya samu munanan raunuka kuma an kai shi wani asibiti mai zaman kansa a yankin, yayin da babura da wuraren hutawa na karkashin bishiyar suka lalace."

Ya kara da cewa kasancewar Amotekun a wurin da abin ya faru shine hana tarzoma da sace kayan 'yan kasuwa a kasuwar.

Dalilin faduwar bishiryar

Shugaban yankin ci gaban Karamar Hukumar Sooro, Oke-Isiwin, Oyo, Seun Oguntona, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na NAN cewa wadanda abin ya shafa mutane ne da suka fake a karkashin bishiyar yayin ruwan sama mai karfi.

Ya kara da cewa wadanda ke kasuwanci a karkashin bishiyar za a mayar da su wurin daban.

Ya bukaci mutanen yankin da su kasance a ko da yaushe cikin gida kuma kada su fake a karkashin bishiyoyi lokacin da ake ruwan sama.

Ya karyata jita-jitar cewa itaciyar tsafi ce, ya kara da cewa wanda ya dasa ta ya mutu shekaru 30 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Mista Oguntona ya ce duk da cewa mutumin ya kasance mai riko da addinin gargajiya na “Sango”, ya dasa bishiyar ne don bai wa mutane inuwa.

Duk kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, bai ci nasara ba saboda bai dauki wayar ba sadda aka kirashi, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

A wani labarin, Ma'aikatar tsaro ta musanta ikirarin da ake yadawa cewa mutumin da ke dauke da bindigar AK47 a bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta shi ne minista Bashir Magashi.

Mai taimaka wa Magashi na musamman kan harkokin yada labarai, Mohammad Abdulkadri, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa wanda aka gani a bidiyon shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Muhalli ta Sojin Najeriya (NACEST) ne da ke Makurdi, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

Ya musanta batun ne a jiya Lahadi 3 ga watan Oktoba, inda ya bayyana cewa lallai ba mai gidansa bane.

Abdulkadri ya yi bayanin cewa duba da yanayin ofis dinsa, shugaban na NACEST yana da ikon doka na daukar makami na doka lokacin tafiya, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.