Tsohon gwamnan mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya rasu

Tsohon gwamnan mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya rasu

- Tsohon gwamna a mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya mutu yana da shekaru 77 a duniya

- A lokacin yana soja, Kanu, ya yi gwamna a jihohin Legas da kuma Imo

- Bayan Kanu ya yi murabus daga aikin soja, ya zama mai rajin kare hakkin bil adama

Tsohon gwamnan jihohin Legas da Imo a zamanin mulkin soja, Rear Admiral Ndubisi Kanu (mai murabus) ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.

Abokiyar huldar Kanu kuma mukusanciyarsa, Mrs Joe Okei-Odumakin ta tabbatar wa The Punch labarin a ranar Laraba.

Tsohon gwamnan mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya rasu
Tsohon gwamnan mulkin soja, Ndubisi Kanu, ya rasu. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

"Tabbas ya rasu. Wannan labari ne na bakin ciki. Za mu fitar da sanarwa nan bada dadewa ba," in ji ta.

A halin yanzu ba a iya tabbatar da sanadin rasuwarsa ba.

Kanu, wadda tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Murtala Mohammed ya nada cikin majalisar kolin sojoji a shekarar 1975, daga bisani ya zama mai rajin kare hakkin bil adama bayan barin aikin soja.

KU KARANTA: Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da 'yan bindiga a Katsina

Ya shiga kungiyar kare demokradiyya ta NADECO, sannan ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin an soke zaben shugaban kasa na June 12 a shekarar 1993.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164