Da Duminsa: Ka gaggauta ayyana yan fashin daji a matsayin yan ta'adda, Majalisar wakilai ga Shugaba Buhari

Da Duminsa: Ka gaggauta ayyana yan fashin daji a matsayin yan ta'adda, Majalisar wakilai ga Shugaba Buhari

  • Majalisar wakilan tarayya ta bi bayan majalisar dattijai wajen kira ga shugaba Buhari ya ayyana yan fashi a matsayin yan ta'adda
  • A zaman majalisar na ranar Alhamis, shugaban kwamitin tsaro, Babajimi Benson, ya gabatar da bukatar goyon bayan matakin sanatoci cikin gaggawa
  • Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya tambayi mambobi ko akwai mai jayayya, amma baki ɗayansu suka tabbatar da amincewa

Abuja - Yan majalisar wakilan tarayyan Najeriya sun goyi bayan matakin yan uwansu na majalisar dattijai kan ayyana yan fashi a matsayin yan ta'adda.

Punch ta ruwaito cewa Majalisar wakilai ta yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gaggauta bayyana yan fashin daji a matsayin yan ta'adda.

Yan fashin daji ko sunan yan bindiga da ake kiran su da shi, sun mamaye yankin arewa maso yamma da kuma wasu yankuna a arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa tun ranar Laraba ne, majalisar dattijai ta ɗauki wannan matakin.

Zauren Majalisar wakilai
Da Duminsa: Ka gaggauta ayyana yan fashin daji a matsayin yan ta'adda, Majalisar wakilai ga Shugaba Buhari Hoto: dailyost.ng
Asali: UGC

Wa ya kai kudirin gaban majalisar wakilai?

Shugaban kwamitin tsaro a majalisar wakilai, Babajimi Benson, shine ya gabatar da kudirin tare da roƙon takwarorinsa su goyi bayan matakin da sanatoci suka ɗauka.

Honorabun Benson, ya gabatar da kudirin a zaman majalisar na yau Alhamis, tare da bukatar gaggauta amince wa da shi.

Shin wasu sun ƙalubalanci kudirin?

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya tambayi mambobin majalisar cewa akwai wanda yake kalubalantar wannan kudiri? Amma baki ɗayansu suka amsa da "Babu!"

Ba tare da jayayya ba, nan take majalisar wakilai ta amince da kudirin tare da kira ga shugaba Buhari ya ayyana wannan matakin kan yan fashi.

A wani labarin na daban kuma Gwamnonin Jam'iyyar PDP Sun Cimma Matsaya Kan Yankin da Zai Fitar da Shugaba

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi ya soki tsarin biyan tallafin fetur, ya fallasa badakalar da ke cikin tsarin

Gwamnonin jam'iyyar PDP sun kaɗa kuri'ar amincewa shugaban jam'iyya na gaba ya fito daga yankin arewacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan wata babbar alama ce dake nuna babbar jam'iyyar hamayya zata kai tikitin shugaban ƙasa yankin kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262