Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

  • ICJI tare da wasu kamfanonin labarai sun jagoranci wani bincike da ya fallasa sirrikan kazantacciyar dukiyar wasu shugabanni a duniya
  • Bincike ya gano takardun da suka bayyana sirrikan tsoffi da sabbin shugabannin 35 na duniya, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91 na duniya
  • Duk wannan harkallar da suke suna samun taimakon Amurka ne da wasu kasashe masu arziki kuma hakan ya na taimakawa wurin sake talauta duniya ne

Miliyoyin takardu sun bayyana kuma gagarumin binciken hadin guiwa na 'yan jarida ya bankado sirrikan dukiyoyin tsoffi da wasu shugabanni a duniya, 'yan siyasa da jami'an gwamnati sama da 330 a kasashe 91 na duniya.

Takardun sirrin sun bayyana wasu harkallar bakin teku na Sarkin Jordan, shugabannin kasashen Ukraine, Kenya da Ecuador, firayim ministan jamhuriyar Czech da tsohon firayim ministan Tony Blair.

Kara karanta wannan

Fallasar handama: An matsa wa Buhari lamba kan ya bincike Bagudu, Obi da sauransu

Takardun sun bayyana yanayin hada-hadar kudin Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin da sama da biloniyoyin duniya 130 na kasashen Rasha, Amurka, Turkiyya da sauran kasashe, Premium Times ta wallafa.

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 a kasashe 91 a duniya
Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 a kasashe 91 a duniya. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Takardun da aka bankado sun bayyana manyan masu karfin iko a duniya da za su iya kawo sauyi amma kuma sai suke karuwa da halin da duniyar ta ke ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Suna dankara kadarori a kamfanoni kuma gwamnatinsu ba ta wani kokarin a zo a gani wurin dakile yawon haramtattun dunkiyoyi da ke azurta 'yan ta'adda tare da talauta kasashen duniya.

Daga cikin boyayyun dukiyoyin da aka bankado takardunsu akwai:

Akwai wani tamfatsetsen gida da ke yankin Faransa mai dauke da silima tare da wurin wanka 2 na dala miliyan 22 wanda firayim jamhuriyar Czech kuma biloniyan da ke yakar rashawa ya siya ta wani kamfani.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Sama da dala miliyan 13 da aka boye a wata harkallar sirri a Amurka daga wasu iyalai masu matukar karfin iko a Guatamela, daular da ke juya duniyar hada sabulai da janbaki da ake zarginsu da cutar da ma'aikatansu da duniya baki daya.

Wasu katafaren gidaje guda 3 da aka siya a Malibu ta hannun wasu kamfanoni uku kan dala miliyan sittin da takwas, mallakin Sarkin Jordan a shekarun da 'yan kasar suka cika titi suna kuka kan rashin aikin yi da rashawa.

Wadannan sirrikan ana kiran su da "Takardun Pandora".

Gagarumin binciken da 'yan jaridan suka yi ya bankado sama da takardun sirri miliyan 11.9 kuma ya samu aikin zakakuran 'yan jarida sama da dari shida daga gidajen jaridu daban-daban wadanda suka kwashe shekaru 2 suna aikin gano wasu sirrika tare da dubo takardun kotu da sauransu a kasashen duniya.

Takardun da aka samu sun fito ne daga wasu ayyukan bakin teku na duniya wadanda aka hada da kamfanonin mai tare da wasu masu son boye harkallar kudadensu a duhu.

Kara karanta wannan

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

Bayanan sun nuna kusan sirrikan tsoffin shugabannin kasashen duniya da na yanzu wanda ba a taba bankado irin shi ba a a duniya.

A wannan zamanin na rashawa, takardun sun samar da bayanan yadda kudi ke kaiwa da kawowa a karni na 21 da kuma yadda ake tankwasa dokoki tare da karya su a duniya wanda Amurka ce ta bada dama da sauran kasashe masu arziki a duniya.

Binciken ICIJ tare da takwarorin ta ya fallasa sirrikan watanda da kudaden da 'yan siyasar duniya suke yi tare kuma da dalilan da yasa gwamnati da kungiyoyin duniya suka kasa kawo karshen wasu matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng