‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

  • Ana fama da kashe-kashe da kone-kone a garuruwan jihar Anambra
  • Akwai yiwuwar ‘Yan kungiyar IPOB ne suke kai wadannan hare-hare
  • A ‘yan kwanakin nan an rasa manyan mutane da ake ji da su a Anambra

Anambra- Jama’a suna cikin halin firgici da rashin aminci a jihar Anambra saboda halin da aka shiga na rikici a dalilin ta’addancin wasu ‘yan bindiga.

Daily Trust tace ana fama da kashe-kashe da ta’adi yayin da ake shirin zaben sabon gwamnan Anambra.

A dalilin abubuwan da ke faru wa, ‘yan siyasa da dama sun boye saboda gudun su fada hannun ‘yan bindigan da ke kashe mutane babu gaira, babu dalili.

An kai wa 'dan majalisa hari

Jaridar tace har zuwa ranar Juma’ar da ta wuce (1 ga watan Oktoba, 2021), an hallaka direban wani ‘dan majalisar tarayya da kuma jami’in ‘dan sanda.

Read also

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Wannan lamari ya auku yayin da ‘yan bindigan suka kona wani ofishin ‘yan sanda da ke Anambra.

Willie Obiano
Gwamnan Anambra, Willie Obiano Hoto: @WillieMObiano
Source: Twitter

‘Yan bindigan sun kai hari ga tawagar ‘dan majalisa mai wakiltar mazabun Nnewi da Ekwusigo a majalisar wakilan tarayya, Hon. Chris Emeka Azubogu.

Honarabul Chris Azubogu wanda ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki a kasa bai cikin motocin a lokacin da aka kai wa tagawarsa hari.

An hallaka Mai dakin Dora Akunyili

Rahoton yace kafin nan an kashe wasu mutane bakwai a garuruwan jihar, daga ciki har da Dr Chike Akunyili, mai gidan marigayiya Farfesa Dora Akunyili.

Farfesa Dora Akunyili ta rike shugabar hukumar NAFDAC, kafin ta zama Ministar yada labarai a gwamnatin Marigayayi shugaban Ummaru Musa ‘Yar’adua.

Har ila yau ‘yan bindiga sun kashe wani tsohon Sarki, Mkpunando na Aguleri watau Alex Edozieuno. An kashe tsohon Mai martaban ne a garin Otuocha.

Read also

Badakala: Sheikh Kalarawy ya ajiye mukaminsa saboda za a gina shaguna a masallacin idi

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala za ta shiga siyasa?

Rahotanni sun zo mana cewa tsohuwar Ministar kudin Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta fara gajiya da aiki a WTO, tana tunanin ta sauka daga mukaminta.

Daga samun kujerar kungiyar kasuwancin ta Duniya, an soma yada labarai tsohuwar Ministar za ta koma siyasa, ta nemi takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Source: Legit

Online view pixel