Ya kamata a tambayi Ahmad Gumi kan yadda yake tuntubar ‘yan fashi – Sanatan APC
- Sanata Mohammed Sani Musa mai wakiltar Neja ta gabas, ya nemi gwamnatin tarayya da ta nuna halin rashin tausayi a kan 'yan fashi
- Musa ya kuma bukaci da a tambayi shahararren malamin Musulunci, Ahmad Gumi kan yadda yake tuntubar 'yan fashin na daji
- Sanatan na APC ya kuma kalubalanci dalilin da yasa Gumi ya gaza samawa gwamnati mafita wajen yakar 'yan fashin
Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar Neja ta gabas, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta nuna ‘rashin tausayi’ a kan 'yan fashi.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sanatan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya fadi haka ne a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba, yayin wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels.
Yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda al’amura suka gudana a mazabarsa da Neja, dan majalisar ya ce jihar ta dan samu zaman lafiya na dan wani lokaci, amma yanzu lamarin ya tsananta.
Ya ce:
“A cikin watanni shida da suka gabata, abin ya munana. Sai lokacin da sabbin shuwagabannin tsaro suka zo sannan aka dauki wani mataki, daban da abin da suke yi a da. Kuma mun samu wani irin zaman lafiya na dan wani lokaci, har zuwa yanzu, lokacin da 'yan ta'adda duk suka koma.
“Da alama dukkansu sun koma Zamfara, wanda da alama ita ce cibiyarta. Don haka, lokacin da duk suka koma Zamfara, kuma gwamnati ta yanke shawarar lallasa su a Zamfara, yanzu suna yaduwa. Mun sami kwanciyar hankali a cikin watanni biyu da suka gabata, amma yanzu, sun dawo kuma sun kasance marasa tausayi. Don haka, muna kuma son gwamnati ta nuna rashin tausayi a kan su.”
Musa ya ce ya kamata a tambayi Ahmad Gumi, babban malamin addinin Islama wanda ya sha yin magana da yawun 'yan fashi kan yadda yake tuntubar su.
Sanatan, wanda ya dage cewa "akwai bukatar ayyana wadannan 'yan fashi a matsayin 'yan ta'adda", ya yi mamakin dalilin da ya sa Gumi bai taimaki gwamnati da bayanai kan magance 'yan fashi ba.
"Ina tuna cewa daya daga cikin shahararrun malaman addinin Musulunci, Sheikh Gumi, ya kasance a wani lokaci yana shiga cikin dazuzzuka don kasancewa tare da wadannan mutane.
"Ina ganin ya kamata a tambayi mutum kamar Gumi yadda yake kira don isa ga waɗannan mutanen. Kuma idan zai iya kaiwa ga waɗannan mutanen, me yasa bai iya taimakawa gwamnati ba don ganin an kashe mutanen nan? ”
Ka ayyana ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda, Majalisar dattawa ga Buhari
A baya mun ji cewa majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar ta kuma shawarci shugaban kasar da ya yi yaki da 'yan bindigar gaba daya, gami da tayar da bama-bamai a duk wuraren da suke don kashe su da kawar da su.
Har ila yau, majalisar ta kuma nemi Buhari da ya bayyana dukkan sanannun shugabannin 'yan bindigar da ake nema ruwa a jallo tare da bibiyar su a duk inda suke don kamawa da gurfanar da su.
Asali: Legit.ng