Ka ayyana ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda, Majalisar dattawa ga Buhari

Ka ayyana ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda, Majalisar dattawa ga Buhari

  • Majalisar Dattawa ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda
  • Ta kuma bukaci shugaban kasar da ya yi yaki da 'yan bindigar gaba daya, gami da tayar da bama-bamai a maboyarsu
  • Matakin ya biyo bayan kudirin da Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir mai wakiltan Sakkwato ta Gabas da wasu mutane takwas suka gabatar

Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar ta kuma shawarci shugaban kasar da ya yi yaki da 'yan bindigar gaba daya, gami da tayar da bama-bamai a duk wuraren da suke don kashe su da kawar da su.

Ka ayyana ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda, Majalisar dattawa ga Buhari
Majalisa ta nemi Buhari ya ayyana ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Har ila yau, majalisar ta kuma nemi Buhari da ya bayyana dukkan sanannun shugabannin 'yan bindigar da ake nema ruwa a jallo tare da bibiyar su a duk inda suke don kamawa da gurfanar da su.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Shawarwarin sun biyo bayan kudirin da Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir (Sakkwato ta Gabas) da wasu takwas suka gabatar.

Gobir ya lura cewa yanzu yankin Sakkwato ta gabas ya zama mafakar 'yan fashi saboda farmakin da ake kai musu a jihar Zamfara.

Ya tuno da kisan da aka yi wa jami’an tsaro 21 a ranar Asabar da ta gabata a Dama da Gangara amma har yanzu ba a iya tantance adadin fararen hular da ke makwabtaka da su ba.

Dan majalisar ya ce babban kisan gillar ya nuna girman matsalar da ya ce tana bukatar hadin kai da matakin gaggawa ta hanyar ayyana yaki da 'yan fashi gaba daya.

Ya nuna damuwar sa cewa rasa irin wannan adadin na kwararrun jami’an zai kara rage karfin adadin jami’an tsaro a kasar, ta yadda zai kawo hadari ga tsarin tsaron kasar.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Ya kuma koka kan cewa mafi yawan 'yan fashin yanzu sun koma kananan hukumomin Sabon Birni da Isa saboda ci gaba da ayyukan soji a yankin Zamfara.

Dan majalisar ya ce yayin da ake ci gaba da fatattakar 'yan fashin a jihar Zamfara, babu wani kwakkwaran mataki da aka dauka a jihar Sakkwato, wanda hakan ya sa ayyukan 'yan bindigar ya dabaibaye ta gaba daya.

A cewarsa, hare-haren da sojoji ke kaiwa yan bindigan ba a tsara shi da kyau ba domin ana hada su ne kawai a jihar Zamfara a maimakon dukkan jihohin da 'yan ta'adda suka lalata.

Majalisar dattijai ta yi tsit na minti daya don karrama jaruman da suka mutu da fararen hula da suka rasa rayukansu a cikin munanan ayyukan barayin.

Majalisar ta kuma umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da su gaggauta bayar da dukkan taimakon da ya dace ga wadanda hare-haren ‘yan ta’adda suka rutsa da su a Sakkwato da sauran sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Amurka ta tattara shaidu 6,700 don tabbatar da laifin Abba Kyari

Miyagun yan bindiga sun farmaki yan sanda sun bude musu wuta, Sun kwace bindigu

A wani labarin, wasu yan bindiga da ba'a gane ko su waye ba sun farmaki yan sanda a wurin binciken abun hawa dake kan hanyar Obasanjo-Itele, karamar hukumar Ado-Odo/Ota, jihar Ogun.

Premium times ta ruwaito cewa maharan sun buɗe wa jami'an yan sandan wuta yayin da suke kan aiki, da misalin ƙarfe 3:11 na rana, ranar Lahadi, inda suka jikkata mutum ɗaya.

Tawagar jami'an yan sandan da aka kaiwa harin, suna ƙarƙashin jagorancin ASP Nasiru Azeez, sufeta Olabisi Lawrence da sufeta Atari Friday.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng