Miyagun yan bindiga sun farmaki yan sanda sun bude musu wuta, Sun kwace bindigu
- Wasu miyagun yan bindiga sun mamayi tawagar jami'an yan sanda sun buɗe musu wuta a wurin binciken abun hawa a jihar Ogun
- Rahoto ya nuna cewa ɗaya daga cikin jami'an yan sandan ya samu raunuka, kuma an gaggauta kai shi asibiti domin kulawa da lafiya
- Sai dai har zuwa yanzun rundunar yan sanda ba ta fitar da sanar wa game da harin a hukumance ba
Ogun - Wasu yan bindiga da ba'a gane ko su waye ba sun farmaki yan sanda a wurin binciken abun hawa dake kan hanyar Obasanjo-Itele, karamar hukumar Ado-Odo/Ota, jihar Ogun.
Premium times ta ruwaito cewa maharan sun buɗe wa jami'an yan sandan wuta yayin da suke kan aiki, da misalin ƙarfe 3:11 na rana, ranar Lahadi, inda suka jikkata mutum ɗaya.
Tawagar jami'an yan sandan da aka kaiwa harin, suna ƙarƙashin jagorancin ASP Nasiru Azeez, sufeta Olabisi Lawrence da sufeta Atari Friday.
Bindigu nawa tsagerun suka kwace?
Ɗaya daga jami'an yan sanda ya shaidawa manema labarai cewa, "Hukumar yan sanda ba ta son cewa komai duk da maharan sun yi awon gaba da AK-47."
Ɗan sandan, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace, "Bindigar da aka kwace tana da lamba 804611, da kuma alburusai 30."
"Jami'in ɗan sanda guda ɗaya da ya samu rauni yayin harin an yi gaggawar kai shi asibitin jiha dake Ota, domin kulawa."
"Maimakon hukumar yan sanda ta sanar da halin da ake ciki, domin mutane su sani, ƙila a gano maɓoyarsu, amma ta yi shiru, ta ƙi cewa komai kan lamarin."
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, bai amsa ko ɗaya daga cikin jerin kiran wayar da aka masa ba.
A wani labarin kuma Wani Matashi Dan Shekara 25 Ya Hallaka Mahaifiyarsa Saboda Abinci
Rundunar yan sanda reshen jihar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan shekara 25, Solomon, bisa zargin kashe mahaifiyarsa.
Rahoton yan sanda ya nuna cewa wanda ake zargin ya tura mahaifiyar tasa ne cikin rijiya saboda tace masa babu abinci a gida.
Asali: Legit.ng