Jerin sunaye: BudgIT ya bayyana jihohin Najeriya 5 mafi kokari a 2021

Jerin sunaye: BudgIT ya bayyana jihohin Najeriya 5 mafi kokari a 2021

BudgIT, wani kamfani na fasaha da ke bayani dalla-dalla kan lamuran da suka shafi kudi, a ranar Laraba, 29 ga Satumba, ya fitar da rahotonsa na shekara wanda ke bayyana jihohi mafi kokari kuma mafi gazawa a Najeriya.

A cikin rahoton, kamfanin ya bayyana cewa jihohi biyar sun fito a matsayin waɗanda suka haɓaka kokarinsu ta bangaren kuɗi da matakan dorewa.

Kamfanin ya yi bayanin cewa rahotonsa ya yi la’akari ne da kudaden shiga na jihohi (IGR) wanda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta wallafa.

Jerin sunaye: BudgIT ya bayyana jihohin Najeriya 5 mafi kokari a 2021
Rahoton ya fito ne daga wallafar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) Hoto: NGF
Asali: Facebook

Ya kara da cewa yayin bincikensa, an yi amfani da sigogi hudu don duba lafiyar kasafin kudi na jihohin a cikin wannan lokacin.

Da yake bayyana wadannan sigogi guda hudu, Babban Daraktan BudgIT Gabriel Okeowo, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

“Ga rahoton bana, mun binciki lafiyar kasafin kudin jihohi ta hanyar amfani da ma'aunai huɗu wato; ikon jihohi wajen cimma aikinsu tare da IGR da VAT, ikon jihohi wajen daukar nauyin ayyukansu da biyan bashi tare da jimillar kudaden shigar su, kasafin kuɗin nawa jihohi ke da shi da za su iya ciyo ƙarin bashi, da matakin kowace jiha dangane da kudaden aikin su."

Ga jerin jihohi biyar da suka sarrafa dukiyoyin su fiye da sauran a ƙasa:

1. Rivers

2. Lagos

3. Anambra

4. Ebonyi

5. Kebbi

Yayin da ukun farko su kaɗai ne za su iya rayuwa a kan IGR da Harajin kayayyaki (VAT), biyun ƙarshe - Ebonyi da Kebbi - sun samu shiga ne a matsayin sabbin shiga rukunin manyan jihohi 5 saboda rawar da suka taka.

Da yake magana kan ci gaban kowannensu, rahoton ya bayyana:

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

“Jihar Ebonyi ta haɓaka IGR dinta da kashi 82.3 bisa ɗari daga naira biliyan 7.5 a shekarar 2019 zuwa biliyan 13.6 a shekarar 2020, yayin da jihar Kebbi ta haɓaka kuɗin shigarta da kashi 87.02 bisa ɗari daga biliyan 7.4 a shekarar 2019 zuwa biliyan 13.8 a 2020. A halin yanzu, Jihar Ogun (yanzu ta 19) da jihar Kano (yanzu ta 22), sun fice daga cikin manyan rukunin 5 saboda raguwar IGR a 2020.”

Jerin Jihohi 6 da za su iya tsayawa kan kafafunsu ba tare da kowani tallafi daga tarayya ba

A halin da ake ciki, Ƙididdigar yanayin dorewar rayuwar jihohi na shekara-shekara (ASVI) wanda mujallar Economic Confidential ke wallafawa, ya bayyana wasu jihohi da za su iya rayuwa ba tare da samun kasafin kudin wata-wata daga asusun gwamnatin tarayya ba.

ASVI ta auna yanayin dorewar rayuwar jihohin ne ta hanyar la'akari da kudaden shigar da kowacce jiha ke tarawa (IGR), kason da take turawa asusun gwamnatin tarayyar a kowacce shekara.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohi 6 da za su iya tsayawa kan kafafunsu ba tare da kowani tallafi daga tarayya ba

Legit.ng ta tattaro cewa jihohin da ke da IGR kasa da kashi 10% na jimillar kudaden da suke karba daga gwamnatin tarayya sune ake dauka a matsayin wadanda ba za su iya tsayuwa da kafafunsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel