Jerin Jihohi 6 da za su iya tsayawa kan kafafunsu ba tare da kowani tallafi daga tarayya ba

Jerin Jihohi 6 da za su iya tsayawa kan kafafunsu ba tare da kowani tallafi daga tarayya ba

Ƙididdigar yanayin dorewar rayuwar jihohi na shekara-shekara (ASVI) wanda mujallar Economic Confidential ke wallafawa, ya bayyana cewa, akwai wasu jihohi da za su iya rayuwa ba tare da samun kasafin kudin wata-wata daga asusun gwamnatin tarayya ba.

A cewar jaridar The Cable, kididdigar ASVI ta auna yanayin dorewar rayuwar jihohin ne ta hanyar la'akari da kudaden shigar da kowacce jiha ke tarawa (IGR), kason da take turawa asusun gwamnatin tarayyar a kowacce shekara.

Jerin Jihohi 6 da za su iya tsayawa kan kafafunsu ba tare da kowani tallafi daga tarayya ba
Legas, Ribas, Ogun, Kaduna, Oyo da Anambra za su iya rayuwa ba tare da kasafi na tarayya ba. Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Nyesom Wike, Prince Dr Dapo Abiodun, Nasir El-Rufai, Seyi Makinde, Willie Obiano
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa jihohin da ke da IGR kasa da kashi 10% na jimillar kudaden da suke karba daga gwamnatin tarayya sune ake dauka a matsayin wadanda ba za su iya tsayuwa da kafafunsu ba.

A kasa ga jerin jihohin da aka lissafa a matsayin waɗanda za su iya rayuwa ba tare da tallafi daga gwamnatin tarayya ba:

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

1. Jihar Lagos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Jihar Rivers

3. Jihar Ogun

4. Jihar Kaduna

5. Jihar Oyo

6. Jihar Anambra

A cewar rahoton, jihohin da aka lissafa a nan za su iya rayuwa ba tare da tallafin tarayya ba saboda suna samar da kuɗaden shiga masu yawa a cikin gida.

Misali, a shekarar 2020 Legas ta karbi naira biliyan 299 a matsayin kudaden da gwamnatin tarayya ta ware mata amma ta samar da biliyan N418 a cikin gida (139%).

Hakanan, jihar Ribas wacce ta samar da IGR na naira biliyan 117 ta samu N198 biliyan a matsayin kason tarayya (58%).

Dangane da Ogun, jihar kudu maso yamma ta samar da biliyan N50 a matsayin IGR idan aka kwatanta da kason da gwamnatin tarayya ta ware mata na naira biliyan 88 (57%).

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

Jihar Kaduna ta samar da Naira biliyan 50 a cikin gida yayin da kasonta na asusun gwamnatin tarayya ya kai Naira biliyan 124 (kashi 40%).

Jihar Oyo da ke da IGR na biliyan 38 ta sami Naira biliyan 127 a matsayin kason tarayya (29.7%) yayin da Anambra ta samar da Naira biliyan 28 idan aka kwatanta da Naira biliyan 94 (29.6%) da aka ware mata na tarayya.

Shugabannin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna don tattauna matsalolin yankin

A wani labarin, mun ji cewa shugabannin yankin Arewacin Najeriya sun taru a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin tsaro, zaman lafiya da cigaba da suka addabi yankin.

Wadannan shugabanni sun hada da gwamnonin jihohin Arewa 19 karkashin jagorancin gwamnan Plateau, Simon Lalong; da Shugaban Sarakunan gargajiyan Arewa, Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar Sa'ad.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya karbi bakuncinsu ne ranar Litnin, 27 ga watan Satumba, 2021, a farfajiyar taron gidan gwamnatin Kashim Ibrahim.

Kara karanta wannan

Jerin jihohi 8 da ba za su iya rayuwa ba tare da tallafi daga asusun Gwamnatin Tarayya ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel