Rundunar Yan Sanda Ta Saki Sabon Bayani Kan Shirin Ɗaukar Sabbin Ma'aikata 20,000

Rundunar Yan Sanda Ta Saki Sabon Bayani Kan Shirin Ɗaukar Sabbin Ma'aikata 20,000

  • Hukumar yan sanda ta bayyana cewa ba da jimawa ba zata fara shirin ɗaukar sabbin kananan jami'ai 20,000
  • Sufeta janar na yan sandan ƙasar nan, IGP Usman Baba, yace duk wasu matsaloli da suka sa jinkirin ɗaukar jami'an an ci ƙarfin su
  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, yace ya zama wajibi a cigaba da nuna goyon baya ga jami'an yan sanda

Ibadan, Oyo - Sufeta janar na rundunar yan sandan ƙasar nan, Usman Alkali Baba, yace nan gaba kaɗan za'a fara ɗaukar ƙananan jami'ai 20,000, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

IGP ya yi wannan furuci ne ranar Talata da yamma, yayin da yakai ziyarar aiki ga gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, a Ibadan.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Baba ya shaidawa gwamnan cewa rundunar yan sanda ta shirya ƙara wa jami'anta ƙarfi ta hanyar ɗaukar sabbin kurata.

IGP Usman Alkali Baba
Rundunar Yan Sanda Ta Saki Sabon Bayani Kan Shirin Ɗaukar Sabbin Ma'aikata 20,000 Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Ya ƙara da cewa hukumar yan sanda ta samu nasarar warware duk wasu matsaloli da suka sa jinkirin ɗaukar sabbin jami'an, kuma tuni shugaba Buhari ya amince da shirin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kowane yanki zai amfana

Sufetan yan sandan yace kowace ƙaramar hukuma zata amfana da sabbin kananan jami'ai da za'a ɗauka.

Kowane mutum da aka ɗauka zai yi aiki ne a ƙaramar hukumarsa da yake zaune, a cewar IGP Usman Baba.

Bugu da ƙari, IGP yace shirin ɗaukar jami'an yana da alfanu sosai kuma zai taimaka wa tsarin tsaro na kowane yanki.

Menene maƙasudin ziyarar IGP?

Sufetan yan sandan yace ya kawo wannan ziyarar aikin ne domin ganawa da jami'an yan sanda da kuma kara musu karfin guiwa bayan zanga-zangar EndSARS.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Ya kuma bukaci gwamnan jihar da ya cigaba da goyon bayan jami'an yan sanda da kuma tallafa musu a aikin su.

Yan sanda suna kokari - Gwamna Makinde

Da yake nasa jawabin, Gwamnan Oyo, Makinde, ya bayyana cewa jami'an yan sandan jihar na yin iyakar bakin kokarinsu, haɗa kai da mutane da sauran hukumomin tsaro.

Gwamnan yace:

"Mun san cewa wannan lokaci ne mai matukar wahala da ƙalubale a ƙasar nan, babu isassun kuɗaɗe kuma ga tarin matsaloli."
"Saboda haka ya zama wajibi a gare mu, mu cigaba da goyon bayan namijin kokarin da rundunar yan sanda take yi."

A wani labarin kuma Dan majalisar wakilan tarayya ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Wani ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Benuwai ya bayyana sauya shekarsa daga Labour Party (LP) zuwa APC mai mulki.

Godday Samuel Odagboyi, mai wakiltar Apa/Agatu yace ya ɗauki wannan matakin ne saboda rikicin cikin gida da ya addabi LP.

Read also

Miyagun yan bindiga sun farmaki yan sanda sun bude musu wuta, Sun kwace bindigu

Source: Legit.ng News

Online view pixel