Da Duminsa: Dan majalisar wakilan tarayya ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Da Duminsa: Dan majalisar wakilan tarayya ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

  • Wani ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Benuwai ya bayyana sauya shekarsa daga Labour Party (LP) zuwa APC mai mulki
  • Godday Samuel Odagboyi, mai wakiltar Apa/Agatu yace ya ɗauki wannan matakin ne saboda rikicin cikin gida da ya addabi LP
  • Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya karanta wasikar sauya shekan a gaban mambobin majalisa ranar Talata

Abuja - Dan majalisar wakilan tarayya, Godday Samuel Odagboyi, ya bayyana ficewarsa daga Labour Party (LP), ya koma jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kakakin majalisar wakilai ta ƙasa, Femi Gbajabiamila, shine ya sanar da sauya sheƙar Odagboyi a zaman majalisa na yau Talata, a babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa Odagboyi ya fito ne daga jihar Benuwai, kuma yana wakiltar mazaɓar Apa/Agatu a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Dan majalisar wakilan tarayya ya koma APC
Da Duminsa: Dan majalisar wakilan tarayya ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Meyasa ya ɗauki wannan matakin?

Samuel Odagboyi, ya bayyana cewa ya ɗaukin matakin komawa jam'iyyar APC ne saboda rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa a tsohuwar jam'iyyarsa LP.

"Na kammala rijista da jam'iyyar All Progeressive Congress (APC), har na fara ayyukan cikin gida na jam'iyya."
"Na ɗauki matakin komawa jam'iyyar APC ne saboda rikicin da yaƙi ƙarewa a tsohuwar jami'iyya ta wato LP."

Na gamsu da jagorancin APC

A cikin takardar sauya shekar da kakakin majalisa ya karanta a gaban sauran mambobi, Ɗan majalisan yace ya gamsu matuƙa da jagorancin APC tun sanda aka rantsar da sabuwar majalisa.

A cikin yan makonni kaɗan da suka shuɗe, ana cigaba da samun masu sauya sheƙa a majalisar wakilai.

Kawo yanzun jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan, ta samu ƙaruwar yan majalisar wakilai 11 a cikin watanni hudu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

A wani labarin na daban Yan Najeriya ba zasu iya rayuwa shekara 40 cikin kangin talauci ba, PDP ta caccaki Sheriff

Jam'iyyar hamayya PDP ta faɗawa tsohon gwamnan Borno , Ali Modu Sheriff, cewa ya daina mafarkin APC zata cigaba da mulki har na tsawon shekara 40, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Jam'iyyar PDP, yayin da take martani kan kalaman Sheriff, ranar Litinin, ta hannun sakataren watsa labaranta, Kola Ologbondiyan, tace yan Najeriya sun riga sun dawo daga rakiyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel