Gwamnatin Buhari ta fara bin coci don yiwa masu bautar ranar Lahadi riga-kafin Korona

Gwamnatin Buhari ta fara bin coci don yiwa masu bautar ranar Lahadi riga-kafin Korona

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta fara kai allurar riga-kafin Korona zuwa coci a Najeriya
  • Ta kuma yabawa wasu shugabannin CAN bisa goyon bayan da suka bayar na yin allurar a coci
  • Hakazalika, ga mambobin coci, gwamnati ta yaba musu wajen ba ta hadin kai don cimma burin yin riga-kafin

Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Talata 14 ga watan Satumba ta sanar da shirinta na daukar allurar riga-kafin Korona zuwa cibiyoyin bauta ta Kiristoci, Punch ta ruwaito.

Babban Darakta na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib, ya bayyana hakan ne yayin wayar da kan shugabannin Kiristoci kan kashi na biyu na riga-kafin Korona a babban birnin tarayya Abuja.

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari ta fara kai wa coci riga-kafin Korona
Allurar riga-kafin Korona | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Ya ce:

“Mai martaba, Shugaban CAN, fitattun shugabannin Kirista, mata da maza, ina mai farin cikin sanar da ku cewa daga wannan mataki na 2 na riga-kafin Korona, mun gabatar da allurar riga-kafin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Sojin Najeriya sun kera motocin da kan iya hango 'yan ta'adda daga nisan tazara

“An yi wannan ne don tabbatar da membobin Kiristoci da watakila ba su sami damar yin allurar riga-kafi ba saboda wani dalili an ba su damar yin allurar riga-kafin a wuraren bautarsu.
"Dole ne in fadi cewa sakamako daga coci yana da kyau sosai kuma ina godiya ga dukkan shugabannin Kiristocin da suka ba kungiyar allurar riga-kafin damar zuwa majami'un su da membobin su don samun allurar Korona yayin bautar ranar Lahadi.

Gwamnan Najeriya ya ba ma’aikata wa’adin kwanaki 14 don yin allurar korona

Gwamna Rotimi Akeredolu ya umarci ma’aikatan gwamnati a jihar Ondo da su yi rigakafin COVID-19 a cikin makonni biyu.

An bayar da wannan umarnin ne a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba, a cikin wata takardar da OJ Afolabi, babban sakatare, mai kula da harkokin hidima ya sanya wa hannu, a madadin shugaban ma’aikatan gwamnati na Ondo, jaridar ThisDay ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Gwamnatin ta bayyana cewa daga yanzu ma’aikatan gwamnati za su bayar da katunan shaidar rigakafi kafin a ba su damar shiga wasu wuraren.

Sanarwar tace:

''Gwamnatin jihar Ondo ta sanya allurar rigakafin COVID-19 ya zama tilas ga dukkan ma'aikatan jihar.
“A cikin daftarin gwamnati wanda Sakataren dindindin na harkokin ma’aikaya, Mista O.J. Afolabi, a madadin shugaban ma’aikata, gwamnatin jihar ta ba ma’aikatan gwamnati a jihar makonni biyu su dauki allurar rigakafin.”

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

A wani labarin na daban, Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bazu.

A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.

Kara karanta wannan

Bincike: Sojojin da suka hambarar da mulki a Guinea sun samu horon Amurka

A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.