Shugabannin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna don tattauna matsalolin yankin

Shugabannin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna don tattauna matsalolin yankin

  • Gwamnoni da Sarkunan Arewa sun shiga ganawa a Kaduna don tattauna lamarin Arewa
  • Taron ya samu halartan kusan dukkan masu fada a ji a Arewa
  • Daga cikin lamuran da za'a tattauna akwai lamarin kudin harajin VAT

Kaduna - Shugabannin yankin Arewacin Najeriya sun taru a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin tsaro, zaman lafiya da cigaba da suka addabi yankin.

Wadannan shugabanni sun hada da gwamnonin jihohin Arewa 19 karkashin jagorancin gwamnan Plateau, Simon Lalong; da Shugaban Sarakunan gargajiyan Arewa, Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar Sa'ad.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya karbi bakuncinsu ne ranar Litnin, 27 ga watan Satumba, 2021, a farfajiyar taron gidan gwamnatin Kashim Ibrahim.

Wannan ya biyo bayan ganawar farko da Shugabannin sukayi a watan Febrairu, 2021.

Shugabannin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna don tattauna matsalolin yankin
Shugabannin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna don tattauna matsalolin yankin Hoto: Josiah Jenvulu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ga mulki ga Sarauta: Sarkin Gombe zai naɗa gwamnan jam'iyyar APC Sarauta

Su wa ke hallare yanzu haka a jihar Kaduna?

Daga cikin wadanda ke hallare cikin gwamnoni akwai gwamnan Plateau, Simon Lalong; Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, gwamnan Katsina, AMinu Masari; da gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu.

Hakazalika akwai gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum; Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa; gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru; gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, dss.

Sarakunan Arewa kuma akwai Mai alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad; Shehun Borno, Etsu Nupe, dss.

Shugabannin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna don tattauna matsalolin yankin
Shugabannin Arewacin Najeriya sun hadu a jihar Kaduna don tattauna matsalolin yankin Hoto: Josiah Jenvulu
Asali: Facebook

Wa ke jagoran zaman?

Gwamnan Plateau wanda ke jagorantar zaman ya bayyana abubuwan da zasu tattauna kai wannan karon.

A jawabin da ya saki a shafin sakataren yada labaransa a Facebook, Lalong yace sun taru ne domin samun rahotanni daga kwamitocin da suka nada a Febrairu don duba matsalar tsaron da yankin ke fama da ita.

Yace:

"Zamu duba irin abubuwan da muka samu yi wajen dakile tsagerun yan bindiga, garkuwa da mutane, ta'addanci da kuma sanin abinda zamu yi nan gaba."

Kara karanta wannan

Duka Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su yi muhimmin taro a kan batun harajin VAT

"Hakazalika, zamuyi dubi kan wasu lamurorin da suka taso a fadin tarayya makonnin baya domin fitar da matsayinmu. Daga cikinsu akwai lamarin kudin harajin VAT."

Asali: Legit.ng

Online view pixel