Mutane da dama sun hallaka yayin da miyagun yan Bindiga suka farmaki barikin Sojoji a Sokoto
- Wasu miyagun yan bindiga sun kai haro barikin sojoji a jihar Sokoto, inda suka hallaka jami'ai dama
- Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne da safiyar Jumu'a, kuma an nemi wasu sojoji da dama an rasa bayan harin
- Wani jami'in hukumar NSCDC, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kashe a harin harda abokan aikinsa guda uku
Sokoto - Tsagerun yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Sabon Gari, jihar Sokoto, inda suka kashe jami'ai da dama.
Wakilin Dailytrust ya gano cewa barikin sojojin dake a Kauyen Dama, an laƙaba masa suna, "Sansanin Burkusuma."
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai hari sansanin sojojin ne da sanyin safiyar ranar Jumu'a da ta gabata.
Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Idris Muhammad Gobir, ya shaidawa wani mutumi mai suna Ɗanchaɗi, wanda ya tabbatar da kai harin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sojoji nawa maharan suka kashe?
Mutumin ya bayyana cewa maharan sun hallaka mutane da dama, sannan kuma an nemi wasu jami'an soji an rasa bayan harin.
Bugu da ƙari tsagerun sun ƙone motoci guda biyu, sannan suka yi awon gaba da wata guda ɗaya, wacce suka yi amfani da ita wajen jigilar kayan abinci da suka sace a ƙauyen.
Wani sanannen basarake a yankin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa an tura motoci barikin domin ɗakko gawarwakin dakarun dojin da suka mutu a harin.
Basaraken yace
"Motocin sojoji sama da 10 sun bazama cikin jeji domin nemo maharan da kuma ɗaukar fansa kansu."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya tabbatarwa wakilim Dailytrust cewa akwai jami'an hukumarsu uku da harin ya ritsa da su.
"A halin yanzun muna ɗakin ajiyar gawarwaki domin ɗakko gawar su, a yi musu jana'iza."
A wani labarin na daban kuma Miyagun yan bindiga da dama sun sheka lahira yayin da yan sanda da Sojoji suka dakile hari a Zamfara
Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa yan bindiga da dama sun mutu yayin da suka yi kokarin kai hari garin Shinkafi, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Rundunar ta faɗi haka ne yayin da take martani kan rahoton dake yawo cewa an farmaki garin Shinkafi da caji ofis ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng