Tsohon mataimakin gwamna tare da jiga-jigan APC 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Tsohon mataimakin gwamna tare da jiga-jigan APC 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

  • Jam'iyya mai mulkin ƙasar nan ta samu koma baya a jihar Gombe, yayin da jiga-jiganta aƙalla 15 suka koma jam'iyyar PDP
  • Tsohon mataimakin gwamnan Gombe, Lazarus Yoriyo, yace sun ɗauki matakin ficewa daga APC ne saboda abinda ke faruwa a ciki
  • Shugaban PDP reshen jihar, yace yanzun dai ga shi sun dawo gida PDP saboda inda suka koma ya musu zafi

Gombe - Rahoto ya nuna cewa aƙalla jiga-jigan jam'iyyar APC guda 15, tare da magoya bayansu sun koma jam'iyyar hamayya ta PDP a jihar Gombe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Da yake jawabi ga ɗumbin magoya baya a sakateriyar PDP ranar Asabar, tsohon mataimakin gwamna, Lazarus Yoriyo, yace sam baya jin daɗin abinda ke faruwa a cikin APC, kuma ya ga komai.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa jam'iyyar PDP zata lashe manyan zaɓuka a 2023, Mataimakin Gwamna

Yoriyo ya kasance tsohon mataimakin gwamna ga tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje, wanda a yanzun yake sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya.

Jiga-jigan APC sun koma PDP a Gombe
Tsohon mataimakin gwamna tare da jiga-jigan APC 15 sun dauya sheka zuwa jam'iyyar PDP Hoto: bbc.com
Asali: UGC

PDP ta kasance jam'iyyar dake mulki a jihar Gombe gabanin nasarar da gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya a samu a zaɓen 2019.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu jam'iyyar da ta zarce PDP

Yoriyo ya ƙara da cewa PDP ita ce ja gaba a jam'iyyun siyasa idan aka kwatanta da jam'iyyar APC dake jagoranci.

Tsohon mataimakin gwamnan yace:

"Na shiga APC, na ga dukkan abinda ke faruwa a cikinta, abinda ke gudana a APC sam babu daɗi. PDP itace jam'iyyar da ta dace mu dawo."
"Ina kira ga dubbannin magoya bayan mu, su nemi katin zaɓe, kuma su shirya yayin da babban zaɓen 2023 ke kara kusantowa."

A nasa jawabin, shugaban jam'iyyar PDP reshen Gombe, Abnor Kwaskebe, ya yaba wa matakin da masu sauya shekar suka ɗauka.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: An kori shugabar mata, tsohon minista da wasu jiga-jigai a PDP

The Cable ta rahoto shugaban yace

"Gombe ta PDP ce, kuma PDP ta Gombe ce. Yanzun sun sake dawo wa PDP saboda jam'iyyar APC ta musu zafi."

Kwaskebe yace jihar Gombe zata cigaba da zama jihar PDP, ya ƙara da cewa an so yin amfani da filin township stadium amma hukumomi suƙa hana.

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Sokoto ya bayyana matakin da zai ɗauka kan makarantun Almajirai na haddar Alkur'ani

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, yace gwamnatinsa zata gudanar da gyara a ɓangaren makarantun Almajirai

Gwamnan yace babu dalilin da zaisa gwamnatinsa na hana karatun neman ilimin Alkur'ani a jihar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel