Sule Lamido: Najeriya ba zata taɓa cigaba ba, har sai PDP, APC sun daina tunanin mulki
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, ya caccaki jam'iyya mai mulki da kuma jam'iyyarsa ta PDP
- Lamido ya bayyana cewa Najeriya ba zata taɓa fita daga halin da take ciki ba har sai manyan jam'iyyun sun canza tunaninsu kan mulki
- A cewar Lamidu, tun a zaɓen 2019 ya faɗa cewa duk wanda ya samu nasara tsakanin Atiku da Buhari to Najeriya zata samu matsala
Jigawa - Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya zargi manyan jam'iyyun ƙasar nan APC da PDP da jefa Najeriya cikin halim ƙaƙanikayi, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
A wata fira da Channels TV ranar Lahadi, tsohon gwamnan yace matsalolin Najeriya na ƙaruwa ne saboda mugun kwaɗayin mulkin shugabannin APC da PDP, mai makon saka cigaban ƙasa a gaba.
Bugu da kari, jigon PDP, Lamido, ya bayyana cewa dama tun farko ya yi hasashen haka zata faru ƙarƙashin mulkin jam'iyyar APC.
Ba tare da ɗaga wa jam'iyyarsa ƙafa ba, tsohon gwamnan yace jam'iyyar hamayya PDP zata iya ƙara lalata komai matukar aka sa son rai, da ɓangaranci maimakon tunani kan cigaban ƙasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Son kai ya yi yawa a siyasar Najeriya - Lamido
Sule Lamiɗo yace:
"Gwamnonin kudu sun haɗa baki sun ce suna ƙaunar cigaban Najeriya, kuma idan kaduba mahangarsu, zaka ga suna son kansu, komai a baiwa mutanen su."
"Haka nan sauran mutane kowa da nasa irin son ran, ya kamata jam'iyyun siyasa su daina nuna banbanci. Mu daina saka bukatun mu a gaba, mu kalli Najeriya a dunkule."
"Kowa ya maida hankali kan samun madafun iko, har ta kai ga matsayin mance ainihin matsalolin da suka addabi Najeriya."
APC ta baro shiri tun rani -Lamido
"Abinda APC ta yi kenan tun a shekarar 2014, sun faɗi abubuwa da dama game da Najeriya, yanzun sune da madafun iko, wane cigaba aka samu? komai ya ƙara taɓarɓarewa."
"Idan PDP ba ta shiga taitayinta ba, ta cire ɓangaranci, kowa na shi yasani, me yankinsa zai samu, da zaran ta karbi mulki sai ta fi APC lalacewa."
Shin mulkin karba-karba zai iya ceto Najeriya?
Duk da cewa har yanzun PDP ba ta yanke hukunci kan yankin da zai fitar da shugaban ƙasa ba, Lamido ya shawarci jam'iyyarsa ta bar duk mai sha'awa ya nemi takara.
Tshon gwamnan yace tun farko ya hangi, 'gazawar Najeriya' yayin da jam'iyyun APC da PDP suka fitar da yan takararsu a babban zaɓen 2019.
"Tun a 2014, na yi tunanin cewa jam'iyyun nan biyu dake neman ɗarewa mulki, babu wanda Najeriya ce a zuciyarsa."
"Atiku da Buhari suna neman mulki ne saboda kansu, ba wai don yan Najeriya ba, amma suna kiran a zaɓen su."
"Dama na faɗa cewa duk wanda ya samu nasara to Najeriya zata gaza, kuma ya faru, APC ta lashe zaɓe, amma Najeriya ta lalace domin mun rasa abinda ka san mu da shi."
A wani labarin kuma Ga mulki ga Sarauta: Sarkin Gombe zai naɗa gwamnan jam'iyyar APC Sarauta
Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu III, zai naɗa gwamna Inuwa Yahaya na jihar, sarautar 'Ɗan maje,' kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Hukumar dillancin Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa sarkin ya aike da tawagar mutum takwas, karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Muazu, tsohon gwamnan Bauchi , domin sanar da gwamnan, ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng