Jam'iyyar Hamayya PDP ta lallasa APC mai mulki a zaɓen karamar hukumar Kajuru
- Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta lallasa jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen ƙaramar hukumar Kajuru, jihar Kaduna
- Baturen zaɓen yankin, Dakta Ibrahim Dan Maraya, ya bayyana ɗan takarar PDP, Honorabul Ibrahim Gajere, a matsayin wanda ya lashe zaɓe
- A ranar 4 ga watan Satumba, hukumar zaɓen jihar Kaduna ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin jihar
Kaduna - Jam'iyyar hamayya PDP ta lashe zaɓen kujerar ciyaman na ƙaramar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Hakanan kuma, PDP ta lashe kujerun kansiloli guda 9, yayin jam'iyyar APC mai mulki ta lashe kujerar kansila ɗaya tal.
Da yake sanar da sakamakom zaɓen, bauren zaɓen yankin, Dr Ibrahim Dan Maraya, daga jami'ar jihar Kaduna, yace Ibrahim Gajere na PDP ya samu kuri'u 14,432.
Kuma hakan ya bashi nasara kan ciyaman ɗin da ya gabata kuma ɗan takarar APC, Cafra AB Caino, wanda ya samu kuri'u 9,095.
Wa yaci zaɓen ciyaman a Kajuru?
A jawabinsa Baturen zaɓen yace:
"Honorabul Gajere na jam'iyyar PDP, bayan cike dukkan sharuɗɗan da aka shinfiɗa, kuma ya samu kuri'u mafiya rinjaye, ina mai bayyana cewa shine ya lashe zaɓe."
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa har yanzun ba'a bayyana sakamakom zaɓen ƙaramar hukumar Chikun ba.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna, ta gudanar da zaɓen kananan hukumomi a faɗin jihar Kaduna, ranar 4 ga watan Satumba, 2021.
A wani labarin kuma Buhari ya boye wa shugabannin duniya gaskiyar abinda ke faruwa a mulkinsa, Yan majalisa
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, ya yi watsi da jawabin shugaba Buhari a taron majalisar dinkin duniya karo na 76 (UNGA), kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
A jawabin da ya fitar ɗauke da sanya hannunsa, Ndudi Elumelu, a madadin yan majalisun PDP , yace sun yi nazari sosai kan jawabin da Buhari ya gabatar.
Asali: Legit.ng