Gwamna ya bayyana lokacin da wasu gwamnonin PDP zasu sauya sheka zuwa APC

Gwamna ya bayyana lokacin da wasu gwamnonin PDP zasu sauya sheka zuwa APC

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace akwai sauran gwamnonin PDP da yan majalisun tarayya da zasu sauya sheƙa zuwa APC
  • Lalong, wanda shine shugaban gwamnonin APC, ya bayyana cewa APC ta fi kowace jam'iyya, kuma ta zo ne domin kawo canji ga yan Najeriya
  • A cewar gwamnan, hukumar zaɓe ta shirya gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar, kuma da ikon Allah APC zata lashe

Plateau - Gwamna Simon Lalong na jihar Filato , shugaban gwamnonin APC, yace jam'iyyarsa ta fara shirye-shiryen karbar wasu gwamnoni daga jam'iyyar hamayya PDP, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Lalong ya bayyana cewa yana daga cikin gwamnonin da suka yi dana sanin kasancewa a PDP, suka ɓalle daga jam'iyyar a baya, kafin su koma APC.

A cewar shugaban gwamnonin APC, jam'iyya mai mulki ta karɓi mulki ne domin kawo canji ga yan Najeriya.

Read also

Da Dumi-Dumi: Sanata tare da dubbannin mambobin PDP sun sauya sheka zuwa APC mai mulki

Gwamna Simong Lalong na jihar Filato
Gwamna ya bayyana lokacin da wasu gwamnonin PDP zasu sauya sheka zuwa APC Hoto: gazettengr.com
Source: UGC

Lalong ya faɗi haka ne yayin kaddamar da yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC da miƙa tuta ga yan takarar ciyaman 17 a Shendam.

Gwamnatin jihar Filato ta shirya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar 9 ga watan Oktoba, 2021 a faɗin jihar.

Shin jam'iyyar APC ta mutu?

A jawabinsa, gwamna Lalong yace:

"Wasu mutane na yaɗawa cewa jam'iyyar APC ta mutu, amma abinda muka sani shine, babu wani gwamna, sanata ko ɗan majalisar wakilai da ya fice daga APC, ya koma PDP."
"Amma da yawa daga cikin waɗanda na faɗa, har ma da tsofaffin ministoci, sun dawo cikin jam'iyyar APC."

Yaushe wasu gwamnoni zasu koma APC?

Bugu da ƙari, Lalong yace APC ta jima tana shirin karɓar wasu gwamnoni, sanatoci da mambobin majalisar wakilai da zasu sauya sheka zuwa APC.

Read also

Jam'iyyar Hamayya PDP ta lallasa APC mai mulki a zaɓen karamar hukumar Kajuru

Gwamnan yace jam'iyyar adawa ta ɗauki maganar da gwamnatinsa ta yi da wasa, yayin da hukumar zaɓen jihar ta sanar da za'a gudanar da zaɓen kananan hukumomi.

"Wasu mutane suna tsammanin ba zamu gudanar da zaɓen ba, amma na faɗa cewa insha Allah zamu yi zaɓen kananan hukumomi kuma mu lashe baki ɗaya kujerun ciyaman da izinin Allah."

A wani labarin na daban Fasahar 5G zai taimaka wajen rage aikata laifuka, zamu saka shi a Najeriya a 2022, Sheikh Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, yace za'a saka fasahar 5G a Najeriya a watan Janairu, 2022.

Ministan yace fasahar 5G zata taimaka matuƙa gaya wajen kare manyan kayan gwamnati, da kuma cafke masu lalata su.

Source: Legit

Online view pixel