Da Dumi-Dumi: Sanata ya fice daga jam'iyyar adawa PDP, ya koma APC mai mulki

Da Dumi-Dumi: Sanata ya fice daga jam'iyyar adawa PDP, ya koma APC mai mulki

  • Sanata Steven Odey, tare da dumbin magoya bayansa sun sauya sheƙa daga PDP zuwa Jam'iyyar APC mai mulki
  • Sanata Odey ya shafe watanni takwas a majalisar dattijan Najeriya, kafin daga bisani kotu ta tsige shi, kuma ta maye gurbinsa da wani ɗan PDP
  • Manyan jiga-jigan APC a jihar Cross River, cikinsu harda mataimakin gwamna sun halarci taron karbar sanatan

Cross River - Sanata Steven Odey, na jam'iyyar adawa ta PDP, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Odey, wanda aka tsige daga kujerar sanata a watan da ya gabata bayan hukuncin kotu da cewa ba shi PDP ta tsayar takara a zaɓen cike gurbi ba, wanda ya gudana ranar 5 ga watan Disamba, 2020, ya koma APC tare da dubbannin masoyansa.

Read also

Tsohon mataimakin gwamna tare da jiga-jigan APC 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Ya sauya shekar ne a gundumarsa Yache, ƙaramar hukumar Yala a jihar Cross Rivers cikn ƙarshen makonnan.

Sanata Odey ya koma APC
Da Dumi-Dumi: Sanata ya fice daga jam'iyyar adawa PDP, ya koma APC mai mulki Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

Jiga-Jigan APC sun halarci bikin sauya shekar sanatan

Manyan masu faɗa aji na APC a jihar, da suka haɗa da mataimakin gwamna, Farfesa Ivara Ejemot Esu, wanda ya wakilci gwamna Ben Ayade.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban riko na APC, Matthew Mbu Jnr, kwamishinan ƙananan hukumomi da sauran manyan jami'an gwamnati sun halarci taron.

Sanata Odey, ya shafe watanni takwas kafin a majalisar dattijai kafin kotu ta yanke hukuncin maye gurbinsa da sanata Jarigbe A. Jarigbe, na jam'iyyar PDP.

Tsohon sanatan ya gode wa shugabannin APC

Tsohon sanatan ya gode wa shugabannin jam'iyyar APC bisa kyakkyawar tarbar da suka masa cike da soyayya.

Hakanan kuma ya nuna farin cikin bisa yadda dubbannin magoya bayansa suka amince su sauya sheƙa tare da shi zuwa APC.

Read also

2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa

Meyasa ya koma APC?

Ya kuma bayyana cewa ya ɗauki matakin komawa APC ne saboda mutanensa sun bukaci ya yi hakan, yi wa jama'a aiki ba shi da alaƙa da jam'iyyar siyasa, inji shi.

Yace:

"Babban burina da kuma yanayin da nake gudanar da rayuwata shine na yi wa mutane aiki, kuma ba don samun wani sakamako ba."

A wani labarin kuma Jam'iyyar Hamayya PDP ta lallasa APC mai mulki a zaɓen karamar hukumar Kajuru

Jam'iyyar hamayya PDP ta lashe zaɓen kujerar ciyaman na ƙaramar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Hakanan kuma, PDP ta lashe kujerun kansiloli guda 9, yayin jam'iyyar APC mai mulki ta lashe kujerar kansila ɗaya tal.

Source: Legit

Online view pixel