Buhari da hannunsa ya bani lambar waya muna gaisawa amma bai tsinana min komai ba

Buhari da hannunsa ya bani lambar waya muna gaisawa amma bai tsinana min komai ba

  • Wani dan a mutum Buhari ya bayyana bacin ransa da yadda shugaba Buhari ya mace dashi
  • Ya ce, yana daga cikin wadanda suka tallafa Buhari ya hau mulki, amma karshe basu sami komai ba
  • Ya koka kan yadda ya tsinci kansa cikin halin matsanancin talauci duk da irin gudunmawar da ya ba Buhari

Wani dan Najeriya ya bayyana kokensa ga shugaba Buhari, inda ya ce shugaban bai masa komai duk da cewa ya sha wahala wajen yakin neman zaben shugaban kasa.

Mutumin, wanda ya bayyana sunansa da Badamasi Sima Memai ya bayyana a cikin wani bidiyon da ya yi yawo a kafar sada zumunta ta Facebook a shafin Nasara Radio 98.5 FM, inda ya ke nuna rashin jin dadinsa da halin da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Bayan kai karar mahaifiyarsa ga EFCC, dan Ganduje ya tsere zuwa Egypt

Badamasi ya bayyana irin wahalar da ya sha da shi da ire-irensa basu kaunar shugaba Buhari lokacin yakin neman zabe, inda ya ce sun jure watsa musu ruwan zafi da aka yi amma basu saduda akan shugaban ba.

Buhari da hannunsa ya bani lambar wayarsa, amma ku kalli halin da nake ciki
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa, duk wata goyon baya da aka ba shugaban tare dashi aka je wurin amma a karshe, gashi shugaba Buhari bai tsinana masa komai sai ma zagi a cikin al'umma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana shan wahala a kasar nan, inji Badamasi Sima Memai

Ya yi kira da babbar murya cewa, ya kamata shugaba Buhari ya dubi lamurran kasar ya tallafawa wajen kawo saukin rayuwa, inda ya koka kan hauhawar farashin kayayyaki a kasuwa.

Ya bayyana farashin kayayyakin abinci daban-daban, tare da cewa wani kalan abincin kam sai dai mutum ya kalla yace ya taba ci.

Kara karanta wannan

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

A bangare guda da yake bayyana kusancinsa da shugaban, Badamasi ya ce shugaba Buhari da kansa ya bashi lambar waya, amma hakan bai haifar da da mai ido ba.

A cewarsa:

"Ko inuwarka na gani sai na gaisheta, amma yanzu dinnan yau, a lokacin kace a bani lambar wayarka, aka bani lambar wayar, ko da yaushe da zan kira ka mu gaisa.
"Ni Badamasi Sima Memai ni nake kiransa a waya ya daga mu yi ta waya dashi. Amma mai girma shugaban kasa tunda ka kau, ka tarad dani ina da mota uku, ina sayar da mai, ka duba 'yan Neja Delta amma yanzu yau a kasa nake yawo.
"'Yan Neja Delta ka sallamesu mu kungiyar Petroleum Roadside Association mun koma unguwa a zaune ba aikin yi ga iyalai."

A cewarsa, kuma ya yi duk wannan ne domin Allah.

Jama'ar Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke tafiya da kuma yadda farashin kayayyaki ke hauhawa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

Kalli cikakken bidiyon a nan:

Abin kunya ne Najeriya ta ke kiran kanta uwa ga Afrika, inji tsohon sarkin Kano Sanusi II

A wani labarin, Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya ce Najeriya ta rasa kimarta a matsayin uwa a Afirka ga sauran kasashen da suka bunkasa tattalin arzikin su, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanusi ya ce yanzu Najeriya tana bayan sauran wasu kasashen Afirka da yawa idan aka duba ta fuskar ci gaba.

Sanusi wanda ya kasance Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya fadi haka ne a yayin rufe taron Babban Taron Zuba hannun Jari na Kaduna, mai taken, ‘KadInvest 6.0.’

Asali: Legit.ng

Online view pixel