A yunwace jama’a suke, ka yi wani abu kafin su yi wani abu, Dino Melaye ga Shugaba Buhari
- Sanata Dino Melaye ya ja wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kunne a wata wallafar sa
- Sanatan ya yi wallafar ne ta shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram
- A cewar sa mutane su na fama da yunwa, ya kamata Buhari ya yi wani abu kafin su yi
FCT, Abuja - Sanata Dino Melaye ya yi wata wallafa ta shafin sa na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram yana bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara.
Kamar yadda LIB ta ruwaito, ya bukaci shugaba Buhari ya yi gaggawar tallafa wa mutanen Najeriya sakamakon bakar yunwar da take addabar su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
LIB ta ruwaito yadda Melaye ya yi wallafar a shafin sa inda ya ce:
“Shugaba Buhari, ba lallai ka sani ba, akwai korafi da dama da ake yi a tituna. Mutane su na fama da yunwa, tsadar rayuwa ta na azabtar da talakawa. Ka yi wani abu kafin mutane su yi wani abu.”
Sanatan ya dade yana caccakar gwamnatin Buhari
Dama fitaccen dan siyasar ya saba da caccakar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tun ba yau ba.
Sanannen abu ne idan aka ce tsohon sanatan gwani ne wurin son wadaka da kuma hawa kasaitattun motoci kuma ya wallafa su a shafukan sa.
Da farko dai Dino Malaye ya hau kujerar sanata a jihar Kogi ta jam’iyyar PDP, daga bisani ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC, daga baya kuma ya kara komawa jam’iyyar PDP inda ya so ya zarce a kan kujerar sa a zaben 2019.
Abokin takararsa na jam’iyyar APC, Smart Adeyemi ya maka shi a kotu inda ya bayyana rashin gamsuwar sa dangane da zaben.
Daga nan ne kotu ta umarci sake yin zaben wanda Smart ya yi masa mummunan kaye ya maye gurbin sa a kujerar sanatan.
Tun bayan nan Melaye yake wallafa iri-iri wadanda suke janyo cece-kuce a shafukan sada zumuntar zamani tunda dama mutum ne mai mabiya.
Melaye kwararre ne wurin sakin bidiyoyin da su ke janyo surutai iri-iri, misali lokacin da ya dauki bidiyon sa ya amshi farantin gyada ya daura a kan sa yana kwasar nishadi. Bidiyon da ya zaga lungu da sakon kafafen sada zumunta.
FG ta gano kuma ta taka wa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya birki, Malami
A wani labari daban, Antoni Janar na kasar nan kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ce gwamnatin tarayya ta gano kuma ta dakile duk wadanda suke daukar nauyin ta’addanci a kasar nan.
Malami a wata tattaunawa da NAN tayi da shi a birnin New York ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu nasarar gano duk wasu manyan mutanen da suke daukar makudan kudade su na bai wa ‘yan ta’addan Najeriya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Dama AGF tun watan Mayu ya sanar da cewa kotu za ta fara yanke wa kusan mutane 400 da ake zargin su na da alhakin daukar nauyin Boko Haram kuma cikin su akwai manyan mutanen Najeriya.
Asali: Legit.ng