Wata sabuwa: An gano matsugunin gidan rediyon Nnamdi Kanu da ke tunzura tsageru

Wata sabuwa: An gano matsugunin gidan rediyon Nnamdi Kanu da ke tunzura tsageru

  • Gidan talabijin na CNN ya gano inda gidan rediyon da Nnamdi Kanu ke watsa kiyayya yake a birnin Landan
  • An jima ana son sanin inda gidan rediyon na Kanu yake, inda a nan ne yake watsa wasu shirye-shiryensa
  • An kama Kanu, gashi yanzu an gano inda gidan rediyonsa yake yayin da yake fuskantar shari'a a Najeriya

Shekaru da yawa kenan 'yan Najeriya ke neman sanin inda 'Radio Biafra', cibiyar rediyon kafar intanet wanda ke watsa ajandar 'yan haramtacciyar kungiyar IPOB take.

Jiya, gidan talabijin na CNN, ya gano wani titi mai cike da ganye a Peckham, kudu maso gabashin London, adireshin kungiyar ta IPOB kenan, Vanguard ta ruwaito.

Gidan talabijin na CNN ya bayyana wurin a matsayin wurin da ke kusa da birni, yana mai cewa wannan wuri ne da ba a zata ba ga gidan Rediyon Biafra.

Kara karanta wannan

Ku mamaye titunan Abuja, Kungiyar Ohanaeze Worldwide ga IPOB

An gano inda gidan rediyon Nnamdi Kanu da ya shahara wajen tunzura tsageru yake
Shugaban 'yan IPOB, Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Mazi Nnamdi Kanu ya kafa haramtacciyar kungiyar IPOB a 2012 inda kuma ya kafa Rediyon Biafra a 2009. An kirkiro kungiyar ne domin maido da fafutukar kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma kirkiro 'Radio Biafra' don yadawa, fadakarwa, ilimantarwa, sanarwa da sukar ayyukan gwamnatin Najeriya da Kanu ke yi.

Gwamnatin Tarayya ta haramta kungiyar IPOB a shekarar 2017. Amma kafin nan, a ranar 19 ga watan Oktoba, 2015, an kama Kanu da laifin cin amanar kasa, tayar da zaune tsaye, da tayar da fadan kabilanci. An sake shi bisa beli a 2017 kuma ya gudu zuwa Burtaniya.

Kungiyar IPOB ta soki gwamnatin tarayyar Najeriya kan rashin saka hannun jari mai kyau, nisantar siyasa, rabon albarkatun kasa, nuna wariya, yawan sojoji, kashe-kashe a yankin Kudu maso Gabas, Kudu maso Tsakiya da sassan yankunan Arewa ta Tsakiya na kasar.

Kara karanta wannan

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

An sake kama Kanu a baya-bayan nan a kasar Keyan inda aka kunso shi zuwa Najeriya don fuskantar tuhumar da ake masa.

Gwamnatin Buhari ta ce bata gama da Igboho ba, akwai sabbin tuhume-tuhume a kansa

Biyo bayan da wata kotu a jihar Oyo ta umarci a bai wa Sunday Adeyemo (Igboho) Naira biliyan 20, gwamnatin tarayya ta yi nuni da yiwuwar daukaka kara kan hukuncin.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya Abubakar Malami, ya shaida wa manema cewa gwamnati na da damar daukaka kara kan hukunci ko kuma ta shigar da sabon tuhuma kan dan awaren Yarba Sunday Igboho, rahoton Premium Times.

Ya bayyana haka ne a yau Alhamis, 23 ga watan Satumba, 2021.

Malami ya yi bayanin cewa a cikin yanayin yin biyayya ga umarnin doka akwai wasu hakkoki da bukatun da ke hannun gwamnati, Punch ta kara da cewa.

FG ta ki halartar kotu don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta

Kara karanta wannan

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

A wani labarin, Babbar kotun jihar Abia a ranar Talata ta dage sauraron karar da ta shafi jagoran IPOB da aka tsare, Nnamdi Kanu zuwa 7 ga Oktoba, 2021, Punch ta ruwaito.

Alkalin kotun, Jastis KCJ Okereke, ya dauki wannan mataki ne yayin da fg da wasu mutane biyar da ake kara a shari’ar suka gagara gabatar da bayanansu kan karar da Kanu ya shigar gaban kotun, inda yake kalubalantar take hakkin sa da Gwamnatin Najeriya ta yi.

A cikin karar mai lamba HIH/FR14/2021, wadanda ake kara sun hada da Gwamnatin Tarayyar Najeriya (1), Babban Lauyan Tarayya (2), Babban Hafsan Sojoji (3), Sufeto Janar na 'Yan sanda (5), ​​Darakta Janar , Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (7) da wasu manya uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel