APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

  • Rochas Okorocha yana ganin APC za ta daidaice idan ta ba Arewa tikiti a 2023
  • Tsohon Gwamnan na Imo yace lokaci ya yi da ‘Dan kudu zai karbi mulkin kasar
  • Sanatan yana goyon bayan matsayar da kungiyar Gwamnonin Kudu ta cin ma

Abuja - A ranar Litinin, 20 ga watan Satumba, 2021, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya fara nuna tsoronsa game da kai takara Arewacin Najeriya.

Jaridar Punch ta rahoto Rochas Okorocha yana cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta bangare kaca-kaca, muddin aka hana ‘yan kudu tikitin shugaban kasa,

Sanata Rochas Okorocha ya kuma ba gwamnati shawarar yadda za ta shawo kan matsalar ta da shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

An rahoto Okorocha ya na kira ga gwamnati ta janye kararta da Nnamdi Kanu, ayi sulhu a wajen kotu.

Kara karanta wannan

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

NUJ ta shirya bikin Owelle @ 59

Okorocha mai wakiltar Imo ta yamma a majalisar dattawa ya bayyana wannan ne wajen bikin cika shekara 59 da kungiyar ‘yan jarida suka shirya masa a Abuja.

Rochas Okorocha
Sanata Rochas Okorocha Hoto: Rochas Okorocha
Asali: Facebook

Kungiyar NUJ ta reshen birnin tarayya Abuja ta shirya bikin Owelle @ 59, inda ta yi amfani da wannan dama ta nemi jin ta bakin tsohon gwamnan na jihar Imo.

“Babu dalilin da zai sa APC ta fitar da takarar shugaban kasa daga Kudancin Najeriya. Idan aka ba Arewa tikiti, wannan zai raba kan jam’iyyar.”
“Lokacin da na shigar da APGA cikin APC, babu sunayen da ba a kira ni ba a Kudu maso gabas.”

Ina tare da Gwamnonin Kudu - Okorocha

“Mu zama masu kishin-kasa fiye da son ranmu. Hakan ne zai taimaka wa marasa karfi a al’umma. Idan aka yi haka za a samu canji a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

“Ina tare da kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya a kan kai takara kudancin Najeriya.”

Babu zaman lafiya a PDP

A daidai wannan lokaci ne aka ji cewa wata sabuwar rigima na neman ya barka Jam’iyyar PDP a dalilin zaben shugabanni da lissafin wanda za a ba tikitin 2023

‘Yan siyasan Arewa na neman kujerar shugaban kasa, yayin da wasu ‘Yan kudu ke nuna rashin yardarsu, su kadai aka bari suna harin kujerar shugaban jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel