Ku mamaye titunan Abuja, Kungiyar Ohanaeze Worldwide ga IPOB

Ku mamaye titunan Abuja, Kungiyar Ohanaeze Worldwide ga IPOB

  • An nemi ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB) da su daina tursasa dokar zaman gida a kudu maso gabas
  • A cewar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, ya kamata IPOB ta jagoranci almajiranta a zanga-zangar lumana zuwa Abuja
  • Kungiyar ta ce idan membobin IPOB miliyan 60 kamar yadda shugabannin suka fadi za su iya mamaye Abuja, hakan zai tilasta masu bayyana Nnamdi Kanu

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta aika da sako zuwa ga haramtaciyyar kungiyar nan ta 'yan asalin Biafra (IPOB).

Kungiyar ta kabilar Igbo ta nemi kungiyar da aka haramta ta daina tursasa dokar zaman gida a kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

Ku mamaye titunan Abuja, Kungiyar Ohanaeze Worldwide ga IPOB
Ku mamaye titunan Abuja, Kungiyar Ohanaeze Worldwide ga IPOB Hoto: Radio Biafra

Ku tuna cewa kungiyar ta yi barazanar kulle yankin idan gwamnatin tarayya ta gaza gabatar da Nnamdi Kanu, jagoranta, a gaban kotu a ranar 21 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: AMCON ta ƙwace katafaren gidajen tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, Okechukwu Isiguzoro, babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide, ya ce za a tilastawa gwamnatin tarayya bayyana Nnamdi Kanu idan ‘yan kungiyar IPOB miliyan 60 za su iya mamaye Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku tuna cewa Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Ohanaeze a baya tayi kira ga mutane da su yi watsi da dokar zama a gida.

'Yan Majalisa na Kudu sun yi taro a gidan Ekweremadu kan ceto Nnamdi Kanu

A wani labarin, 'Yan majalisar tarayyar na yankin kudancin Nigeria sun kafa kwamiti da za ta bullo da hanyoyin da za a bi domin ceto shugaban kungiyar masu neman kafa Biafra, wato Nnamdi Kanu da a yanzu ya ke tsare, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya

Hakan na cikin sakon bayan taro ne da kwamitin ta fitar bayan taronta a gidan tsohon mataimakin majalisar dattijai, Ike Ekweremadu a ranar Laraba a cewar rahoton na The Punch.

Sakon bayan taron da dukkan 'yan majalisar kudu na yankin suka ratabba wa hannu, ta yi bayanin cewa an yi taron ne 'don tattaunawa kan batun Mazi Nnamdi da kuma yadda za a warware matsalar.'

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng