Jerin shugabannin Afirka mafi tsufa da ke kan mulki, an bayyana matsayin Buhari

Jerin shugabannin Afirka mafi tsufa da ke kan mulki, an bayyana matsayin Buhari

  • Yawancin shugabannin Afrika da ke kan mulki a yanzu suna a tsakanin shekaru 70 da doriya zuwa 80 da ‘yan kai
  • Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari shine na shida cikin shugabannin guda bakwai inda yake da shekaru 78 a duniya
  • Shugaban na Uganda Yoweri Museveni shine na takwas a wannan jerin, inda yake da shekaru 77 a duniya

A Afirka gaba ɗaya, furfura alama ce ta hikima da gogewa, wanda shine dalilin da ya sa yawancin shugabanni a nahiyar suka kasance tsofaffi wadanda cikinsu akwai ƙwararrun masana.

An tattara tare da lissafa jerin shugabannin Afirka na yanzu da suka tsufa a wannan wallafar.

1. Paul Biya (shekaru 88)

Mutum na farko a jerin shine shugaban kasar Kamaru, Paul Biya. An haifi Biya a ranar ga watan Fabrairu 1933 a Mvomeka'a, Ntem, Kamaru na Faransa. A yanzu yana da shekaru 88 kuma shine mafi tsufa a cikin shugabannin bakar fata.

Kara karanta wannan

Tsofaffin shuwagabannin Afirka guda biyu daga ƙasa ɗaya sun mutu cikin ƙasa da mako guda

Jerin shugabannin Afirka mafi tsufa da ke kan mulki, an bayyana matsayin Buhari
Jerin shugabannin Afirka mafi tsufa da ke kan mulki, an bayyana matsayin Buhari Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Hage Geingob (shekaru 80)

An haifi shugaban Namibia, Hage Geingob a watan Agustan 1941.

3. Evaristo Carvalho (shekaru 80)

Ko da yake shekarunsu ɗaya da Geingob (1941), shugaban Sao Tome and Principle, Evaristo Carvalho ya zo a baya saboda an haife shi a watan Oktoba.

4. Alassane Ouattara (shekaru 79)

Shugaba Ouattara na Ivory Coast wanda ke kan mulki tun 2010 an haife shi a ranar 1 ga watan Janairun 1942 a Dimboko.

5. Teodoro Nguema Mbasogo (79)

Na gaba shine Teodoro Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea. An haifi tsohon hafsan sojan a ranar 5 ga watan Yunin 1942 a Acocan, Equatorial Guinea.

6. Muhammadu Buhari (shekaru 78)

An haifi shugaban Najeriya na yanzu a ranar 17 ga Disamba a Daura, jihar Katsina. Yana kan kujerar mulki a karo na biyu bayan ya yi shugabanci a lokacin mulkin soja tsakanin 1984 zuwa 1985.

Kara karanta wannan

Bincike: Jerin kididdigar basussukan da ake bin Najeriya da inda aka karbo su

7. Nana Akufo-Addo (shekara 77)

Na bakwai shine shugaban kasar Ghana. Nana ya kasance shugaban kasa tun 2017. An haife shi a ranar 29 ga Maris 1944 a Accra, babban birnin kasar.

8. Yoweri Museveni (shekaru 77)

An haife shi a ranar 15 ga Satumba 1944 a Ntungamo, shugaban na Uganda shine na takwas a wannan jerin. Kafin ya kai ga zama shugaban kasa, Museveni babban jami'in soji ne.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, ya amince da wasu manyan sauye-sauye a ma’aikatan gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, Folasade Yemi-Esan, shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, ta sanar da cewa an amince da sauya manyan sakatarorin din-din-din guda biyar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar wacce daraktan yada labarai, Mallam AbdulGaniyu Aminu ya sanya wa hannu ta bayyana cewa jami’an da aka sauya wa wajen aiki za su fara sabbin ayyukansu nan take, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na Biliyan 2.3 A Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel