NDLEA ta cika hannu da wani dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na N2.3Bn a Abuja
- Hukumar NDLEA ta sake babban kamu a Abuja ranar Laraba
- Mutumin da aka kama na shirin fita Najeriya da muggan kwayoyi a jirgin sama
- Janar Mohamed Buba Marwa ya jinjinawa jami'an hukumar
Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wani mai suna Okey Eze, kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe, Abuja.
An damke Eze dauke da nadi 350 na hodar Iblis wanda kudin sa ya kai Naira biliyan biyu da digo uku (N2.3bn).
Hadimin shugaban hukumar, Mahmud Isa Yola, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, 22 ga Satumba, 2021.
Yace Eze mai shekaru 38 kuma dan asalin karamar hukumar Oji-River, jihar Enugu ya shiga komar hukumar ne yayin da ake tantance fasinjoji kafin shiga jirgi na Ethiopian airline mai lamba 911 Bamako, Addis Ababa.
Miyagun kwayoyin wanda nauyin su ya kai Kilograms 7.7 an nade su ne a cikin fakiti guda takwas inda ya sanya su a wurare mabanbanta a cikin kayakin da zai yi tafiya da su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa Shugaban hukumar NDLEA, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa ya jinjinawa jami'an hukumar na reshen NAIA wadanda suka yi nasarar cafke mai laifin tare da kwayoyin.
Hotunan tsohon soja mai shekaru 60 da wani da aka kama da wiwi N7.5m maƙare a mota
Dakarun Safe Haven (OPSH), a ranar Talara, 14 ga watan Satumba sun yi nasarar kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi sun kwato wasu ganye da ake zargin wiwi ne da aka kiyasta kudinsa ya kai N7.5m a Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Ishaku Takwa ya ce an boye abin ne cikin wata mota kirar Toyoya Camry mai lamban Legas, KJA 150 EG.
Wadanda ake zargin sun yi ikirarin an dauke su kwangila ne su kai haramtaccen abin Yola, Jihar Adamawa daga jihar Ondo.
Sauran abubuwan da aka kwace daga hannunsu sun kunshi, ganyen wiwii 18 da aka nada, wayoyin salula 2, jakunan tafiya 3, lita daya da jakunan kudin maza dauke da N570.
Asali: Legit.ng