Tsofaffin shuwagabannin Afirka guda biyu daga ƙasa ɗaya sun mutu cikin ƙasa da mako guda

Tsofaffin shuwagabannin Afirka guda biyu daga ƙasa ɗaya sun mutu cikin ƙasa da mako guda

  • A cikin mako guda, Aljeriya ta rasa tsohon shugabanta biyu, Abdelkader Bensalah da Abdelaziz Bouteflika
  • Yayin da Bensalah ya rasu a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, Bouteflika ya mutu a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba
  • A dunkule, tsoffin shugabannin biyu sun kasance a mulki sama da shekaru ashirin kafin shugaban kasar na yanzu, Shugaba Abdelmadjid, ya hau karagar mulki

Aljeriya - Abdelkader Bensalah, tsohon shugaban rikon kwarya na Aljeriya wanda ya jagoranci kasar ta Afirka a shekarar 2019 lokacin da take fama da mummunan rikicin kasa, ya mutu.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a cewar fadar shugaban kasar Aljeriya, Bensalah ya rasu a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, yana da shekaru 80.

Kara karanta wannan

'Yan Taliban sun nemi a basu damar gabatar da jawabi a taron da Buhari ya je a Amurka

Tsofaffin shuwagabannin Afirka guda biyu daga ƙasa ɗaya sun mutu cikin ƙasa da mako guda
Tsofaffin shuwagabannin Afirka guda biyu daga ƙasa ɗaya sun mutu cikin ƙasa da mako guda Hoto: DzVID
Asali: UGC

Bensalah, wanda ya kuma shugabanci majalisar dattijai ta Aljeriya na tsawon shekaru, ya ci gaba da mulki har zuwa lokacin da aka zabi Shugaba Abdelmadjid Tebboune a karshen shekarar 2019.

An tattaro cewa rasuwar Bensalah ta zo ne bayan doguwar gwagwarmaya da wata cuta da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba.

Ana sa ran za a yi jana'izar marigayi shugaban kasar bayan addu'o'i a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, a makabartar El Alia, gabas da tsakiyar Algiers.

Mutuwar Bensalah ta zo ne kasa da kwanaki bakwai bayan da aka ayyana mutuwar wanda ya gada, Abdelaziz Bouteflika, a ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba.

Bouteflika ya mutu shekaru biyu bayan ya sauka daga mukaminsa bayan zanga -zangar da talakawa da sojoji suka yi a fadin kasar bayan labarin shirinsa na tsayawa takara a wa’adi na biyar ya bayyana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta san matsayar bashin $4bn nan da kwana 7, kwamiti zai zauna

Ya ci gaba da rike madafun iko a cikin kasar na akalla shekaru 20 kafin daga bisani ya yi murabus a shekarar 2019 bayan korafe -korafen jama'a da dama daga 'yan kasar wadanda suka gan shi a matsayin mai mulkin kama -karya.

Bayan Bouteflika ya bar ofis, da kyar ake ganin shi a bainar jama'a har zuwa rasuwarsa a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba.

Mutuwar Deby katuwar matsala ce gare mu - Ministan tsaro ya fadi matakan da ake dauka

A wani labari na daban, Ministan harkar tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya yi magana game da kashe shugaban Chadi, Idriss Deby, da aka yi.

Janar Bashir Magashi ya bayyana cewa kisan Idriss Deby zai iya jawo wa Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da Chadi, matsalolin tsaro.

A dalilin haka gwamnatin tarayya ta ce ta inganta tsaro domin a tabbatar da wanzurwar zaman lafiya, kuma ta na bibiyar kasar da ta ke kan iyakarta.

Kara karanta wannan

Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel