Bincike: Jerin kididdigar basussukan da ake bin Najeriya da inda aka karbo su

Bincike: Jerin kididdigar basussukan da ake bin Najeriya da inda aka karbo su

A ranar Talata, 14 ga watan Satumba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da sabuwar bukata domin amincewa da wasu lamuni na bashi a gaban majalisar dattawa.

Shugaban na Najeriya ya nemi amincewar Majalisar Dokoki ta kasa don karbo bashin $4,054,476,863.00, € 710m da kuma tallafin $125m.

A cikin wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya karanta, Shugaba Buhari ya yi bayanin cewa bashin da ake nema zai tallafawa manyan ayyuka a cikin kasafin kudin 2021.

Bincike: Jerin kididdigar basussukan da ake bin Najeriya da inda da aka karbo su
Basussukan Najeriya | Hoto: DMO
Asali: UGC

Jumillar bashin da ake bin Najeriya

Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da dura kan lamarin da zazzafan martani kan matakin shugaban kasa, Legit.ng ta duba tsarin bashin da Najeriya ke ciki a yanzu da kuma wuraren da aka samo basussukan.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na Biliyan 2.3 A Abuja

A cewar Ofishin Kula da Bashi (DMO), hukumar gwamnatin tarayya da aka kafa don daidaita tsarin kula da basussuka, tarin bashin da ake bin Najeriya zuwa ranar 31 ga Maris, 2021, ya kai tiriliyan 33.107 (dala biliyan 87.239).

Inda aka karbo bashin

Takardar ta DMO ta kuma nuna inda aka karbo bashin kamar haka:

Manyan kungiyoyin duniya

  1. Asusun Bayar da Lamuni na Duniya
  2. Gamayyar Bankin Duniya

Bankin Raya Afirka

Bangaren kasashen duniya

  1. China (Bankin Exim na kasar China)
  2. Faransa (Agence Francaise Development)
  3. Japan (Hukumar Hadin Kan Kasa da Kasa ta kasar Japan)
  4. Indiya (Bankin Exim na kasar Indiya)
  5. Jamus (Kreditanstalt Fur Wiederaufbua)

Bangaren 'yan kasuwa

  1. Eurobonds
  2. Diaspora Bond

Asali: Legit.ng

Online view pixel