Bayan sakon majalisar dinkin duniya, an fara gagarumin sauye-sauye a gwamnatin Shugaba Buhari

Bayan sakon majalisar dinkin duniya, an fara gagarumin sauye-sauye a gwamnatin Shugaba Buhari

  • A ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba ne shugaba Buhari ya amince da sauya wa ma’aikata wuri a ma’aikatan gwamnatin tarayya
  • Ma’aikatun da aka yi sauye-sauyen sun haɗa da ta zirga-zirgar jiragen sama, muhalli, wutar lantarki, da ci gaban matasa da wasanni
  • A cewar shugabancin ma'aikatan gwamnatin tarayya, sauye-sauyen zai fara aiki nan take

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, ya amince da wasu manyan sauye -sauye a ma’aikatan gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, Folasade Yemi-Esan, shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, ta sanar da cewa an amince da sauya manyan sakatarorin din-din-din guda biyar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Bayan sakon majalisar dinkin duniya, an fara gagarumin sauye-sauye a gwamnatin Shugaba Buhari
Bayan sakon majalisar dinkin duniya, an fara gagarumin sauye-sauye a gwamnatin Shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Sanarwar wacce daraktan yada labarai, Mallam AbdulGaniyu Aminu ya sanya wa hannu ta bayyana cewa jami’an da aka sauya wa wajen aiki za su fara sabbin ayyukansu nan take, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Pat Utomi yayi magana game da rade-radin sabuwar jam'iyyar siyasa a ranar 1 ga watan Oktoba

Sakatarorin din-din-din da aka sauya wa wajen aiki sun hada da:

1. William Nwankwo Alo na Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya an sauya masa wuri zuwa Hukumar ‘Yan Sanda (PSC)

2. Abel Olumuyiwa Enitan, Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya yanzu an mayar da shi Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama

3. Hassan Musa, Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya a yanzu an mayar da shi Ma'aikatar Muhalli ta Tarayya

4. Nebeolisa Anako, Ma’aikatar Ci gaban Matasa da Wasanni ta Tarayya, yanzu an sake sauya ta zuwa Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya

5. Ismaila Abubakar, Hukumar ‘Yan Sanda (PSC) a yanzu an sake sauya shi zuwa Ma’aikatar Ci gaban Matasa da Wasanni ta Tarayya.

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

Kara karanta wannan

Shekaru 39 da bada kwangila, ba a soma aikin samar da lantarki a tashar Mambila ba

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta fadakar da jama'a da su kara tsaurara matakan tsaro don shirye -shiryen bikin cika shekaru 61 da samun 'yancin kai na kasar.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, a ranar Juma’a, 24 ga Satumba, ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Adeyemi.

Mohammed, ya yi kira ga mazauna Babban Birnin Tarayya da kewayenta da kada su firgita kuma su ci gaba da ayyukansu na halal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel