Katsina: Jami'an hukumar kwastam sun kwace babura 202 daga hannun 'yan bindiga
- Hukumar kwastam ta kasa, reshen jihar Katsina ta ce ta kwace babura 202 wurin 'yan bindiga a cikin watanni biyu
- Kamar yadda shugaban hukumar na jihar, Chedi Wada ya sanar, ya ce ana amfani da baburan wurin kai wa 'yan bindiga ababen bukata
- Ya ce sun kwace baburan a iyakokin kasar nan da ke da hanyoyi a daji kuma tunda suka kwace har yau babu wanda ya zo da niyyar karba
Katsina - Hukumar kwastam ta kasa, NSC, ta kwace babura 202 daga wasu da ta ke zargi da zama 'yan bindiga da masu taimakonsu a jihar Katsina tsakanin watan Augusta zuwa na Satumba.
Mukaddashin shugaban hukumar na jihar Katsina, Chedi Wada, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma'a a jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.
Chedi ya ce baburan da yawansu kirar Boxer da Jencheng ne kuma an kwace su ne a kusa da iyakokin kasar nan da ke daji.
"Mun zargi ana amfani da baburan ne wurin daukan fetur, kayan abinci da kuma kayan sumogal ga 'yan bindiga a daji.
"Da yawa daga cikin jama'ar da muka kwace baburan daga hannunsu sun tsere kuma babu wanda ya zo ya ce a bashi kayan shi," Shugaban kwastam din yace.
Wada ya ce hukumar na aiki ba dare babu rana wurin tabbatar da ba a shigo da duk wani abun da bai dace ko haramtacce cikin kasar nan ta kowacce iyaka a jihar, Daily Nigerian ta wallafa.
"Yaki da 'yan fashin daji, garkuwa da mutane, satar shanu da sauran miyagun laifuka da 'yan ta'adda a jihar nan da kasar nan duk aikinmu ne baki daya.
“Hukumar kwastam kamar kowacce hukumar tsaro ta na da hannu a ciki. Nan a jihar Katsina, za mu tabbatar da cewa mun kai 'yan fashin daji kasa da sauran miyagu," Wada yace.
Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rufe iyakokin Najeriya na sama da shekara daya ya matukar taimaka wa Najeriya, TheCable ta ruwaito.
A watan Augustan 2019 ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin tudun kasar nan kan shigo da miyagun kwayoyi, makamai da kuma abinci daga kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya.
A watan Disamban 2020, Buhari ya bada umarnin bude iyakokin tudu hudu na kasar nan. Bayan watanni kadan da bude su, shugaban kasan ya bayyana damuwarsa kan cewa rufe iyakokin tudun bai tsinana komai ba wurin hana shigo da makamai kasar nan.
Asali: Legit.ng