Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands

Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da sarauniyar Netherlands cewa rufe iyakokin Najeriya ya matukar taimaka wa kasar
  • Buhari ya tabbatar wa da sarauniya Zorriquieta cewa matukar ta sake kawo ziyara, za ta ga yadda aka inganta ababen more rayuwa
  • Shugaban kasan ya ce rufe iyakokin tudu yasa 'yan Najeriya na samar da abincin da za su ci ko a lokacin da annobar korona ta fado

New York - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rufe iyakokin Najeriya na sama da shekara daya ya matukar taimaka wa Najeriya, TheCable ta ruwaito.

A watan Augustan 2019 ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe dukkan iyakokin tudun kasar nan kan shigo da miyagun kwayoyi, makamai da kuma abinci daga kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwastam za ta fara amfani da 'Drone' wajen sintiri da kama haramtattun kayayyaki

Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands
Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A watan Disamban 2020, Buhari ya bada umarnin bude iyakokin tudu hudu na kasar nan. Bayan watanni kadan da bude su, shugaban kasan ya bayyana damuwarsa kan cewa rufe iyakokin tudun bai tsinana komai ba wurin hana shigo da makamai kasar nan.

Bukatar bude dukkan iyakokin kasar nan da 'yan majalisar wakilai 11 suka mika a watan Yunin 2021, 'yan majalisar dattawa sun nuna rashin amincewarsu, TheCable ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzu shugaban kasa ya na New York domin halartar taron majalisar dinkin duniya na 76, ya samu ganawa da Maxima Zorreguieta, sarauniyar Netherlands a ranar Laraba.

Kamar yadda takardar da Femi Adesina ya fitar ta bayyana, Buhari ya bayyana cigaban da aka samu a kasar nan inda ya kara da cewa mulkinsa ya mayar da hankali wurin ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

Shugaban kasan, wanda ya ce akwai iyakoki wadanda suka zo saboda hawa da saukan farashin man fetur, ya ce idan Zorreguieta ta ziyarci Najeriya, za ta ga manyan sauye-sauye idan ta tuna 2017 lokacin da ta ziyarci kasar.

"Idan babu ababen more rayuwa, cigaba zai samu matsala. A don haka ne muka mayar da hankali kan tituna, dogo da kuma wutar lantarki. Muna da tsari mai kyau kuma muna iyakar kokarinmu," Buhari ya ce.

Adesina ya ce, hukuncin shugaban kasa na rufe iyakokin kasar nan ya biyo bayan bukatarsa na manoma su shuka kuma su ci abinda suka girbe.

"Jama'a sun koma gona kuma hakan ya taimaka mana sosai. Mun samar da takin zamani, mun farfado da madatsan ruwa kuma kwalliya ta biya kudin sabulu," Buhari ya ce.

'Yan fashin daji ne ke kewaye da mu, Al'ummar Kaduna sun koka

A wani labari na daban, kungiyar cigaban katafawa ta jihar Kaduna, ACDA ta koka da yadda 'yan fashin daji suka kewaye yankunansu.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, shugaban kungiyar, Dr. Samuel Achie, wanda ya yi jawabi a madadin mazauna yankin, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kasashen ketare da su kawo musu dauki.

Achie ya kara da cewa dubban katafawa an fatattake su daga inda suka tashi kaka da kakanni kuma suna rayuwa yanzu a matsayin 'yan gudun hijira ba tare da wani tallafi daga gwamnatin jihar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel