Yanzu Yanzu: 'Yan sanda sun cafke wadanda suka yi garkuwa da daliban makarantar Bethel guda uku
- An cafke wasu mutane uku da ake zargi da sace dalibai sama da 100 na Bethel a Kaduna
- Frank Mba, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, ya bayyana haka a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba a Abuja
- A cewarsa, an gabatar da wadanda ake zargin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, a Hedikwatar Rundunar
FCT, Abuja - ‘Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane uku da ke da hannu a sace dalibai sama da 100 na makarantar Bethel Baptist, Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba ne ya gabatar da wadanda ake zargin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, a hedikwatar runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS), a Abuja.
Legit.ng ta tattaro cewa wadanda ake zargin, Adamu Bello, Isiaku Lawal da Muazu Abubakar, sun shaidawa manema labarai cewa su 25 ne suka sace daliban.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa sun ce sun gudanar da aikin ne cikin tsananin neman kudi.
Abubakar, wanda ake zargi mai shekaru 27, ya ce:
“Mu ashirin da biyar ne muka gudanar da aikin. Mun yi garkuwa da dalibai 136 kuma na samu sakon N100,000 daga kudin.”
An Cafke Hatsabibin Ɓarawon Shanu Da Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Katsina
A wani labari na daban, hukumar tsaro ta NSCDC ta ce ta damke wani wanda ake zargin barawon shanu ne da wani mai safarar miyagun kwayoyi a jihar Katsina, rahoton Daily Nigerian.
Jami’in hulda da jama’an hukumar na jihar, DSC Muhammed Tukur ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba a Katsina.
A cewar sa, daya daga cikin su shekarun sa 20 kuma mazaunin kauyen Maikaho ne dake karkashin karamar hukumar Jibia, ana zargin sa da satar shanu da kuma bai wa ‘yan bindiga bayanai.
Asali: Legit.ng