Sojin ruwa sun kame buhunnan shinkafar kasar waje da aka shigo da ita Najeriya

Sojin ruwa sun kame buhunnan shinkafar kasar waje da aka shigo da ita Najeriya

  • Jami'an sojin ruwan Najeriya sun kame wasu masu fasa kwabrin shinkafa a yankin Calabar
  • An kama mutanen ne cikin wata kwalekwale tare da buhunnan shinkafa sama da duba daya
  • Tuni rundunar ta sojin ruwa ta mika mutanen ga rundunar kwastam ta Najeriya don bincike

Kuros Riba - Rundunar sojin ruwan Najeriya ta NNSV, ta cafke mutane uku da ake zargi da fasa kwabrin buhunan haramtacciyar shinkafa guda 1,209 ta ruwa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wadanda ake zargin, Humble Edet, Christian Adebayo da Balle Philip sun shiga hannun jami’an NNSV ne da ke sintiri a nisan mil biyu na ruwa a yankin kudu maso gabas a Calabar.

Da yake yiwa manema labarai karin haske a tashar jirgin ruwan NNSV a ranar Litinin a Calabar, Kwamandan NNSV, Chiedozie Okehie, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin shigo da kayayyakin da aka haramta shigo dasu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wani sojan bogi dan shekara 28 dauke da bindiga da sauransu

Sojin ruwa sun kame buhunnan shinkafar kasar waje da aka shigo da ita Najeriya
Shinkafar Waje | Hoto: nigerianprice.com
Asali: UGC

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Okehie, ya samu wakilcin Babban Jami'in Operation Lafiya Dole, Clement Ayogu, ta hanyar umurnin Jami'in Tutar da ke Kula da Rundunar Sojojin Ruwa ta Gabas, Rear Adm Sanusi Ibrahim.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“An kama wadanda ake zargin da wani kwalekwalen katako dauke da buhuna 1,209 na shinkafar waje a nisan kilomita 2 na kudu maso gabas na yankin Calabar.
“An cafke wadanda ake zargin a ranar 11 ga Satumba, 2021. Muna mika wadanda ake zargin da shinkafar ga jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya.
“Daga binciken da muka yi, wadanda ake zargin sun shigo da kayayyakin ne daga Kamaru zuwa Najeriya.

Kwamandan bayan haka, ya mika wadanda ake zargi da kayayyakin ga jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya.

'Yan sanda sun cafke 'yan fasa kwabri da mota makare da soyayyun kaji

Kara karanta wannan

Gagarumin matsala ya fara yayin da majalisa ta yi barazanar kama wasu manyan nade-naden Buhari

'Yan sandan New Zealand sun kama wasu mutane biyu da ke kokarin shigo da mota da ke cike da soyayyun kaji zuwa Auckland, The Punch ta ruwaito.

Auckland, birni mafi girma a kasar, yana cikin tsauraran ka'idojin takunkumi na Korona tun tsakiyar watan Agusta, ba tare da an ba kowa izinin shiga ko barin yankin ba.

Duk kasuwancin da ba su da mahimmanci, wanda ya hada da wuraren cin abinci na kan titi, an rufe su a Auckland. Sai dai, sauran yankunan New Zealand na da karancin ka'idoji tare da kusan dukkanin nau'ikan kasuwanci a bude.

'Yan sanda sun ce jami'an da ke sintiri kan hanyoyin da ke kusa da kan iyaka sun lura da motar "abin zargi" tana tafiya a kan lalatacciyar hanyar.

Abun Kunya: Wani Mutumi Ya Dirkawa Diyarsa Yar Shekara 19 Ciki, Yan Sanda Sun Damke Shi

A wani labarin, rundunar yan sanda reshen jihar Ogun ta cafke wani mutumi ɗan kimanin shekara 45, Olaoluwa Jimoh, da zargin ɗirkawa ɗiyarsa ciki a yankin Ode-Remo, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin saman Najeriya ta fara bincike kan barin wuta da jirgin yaki ya yi kan fararen hula a Yobe

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin rundunar yan sandan Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya fitar.

Wani sashin jawabin yace: "Hukumar yan sanda ta damƙe Jimoh a ranar 16 ga watan Satumba bisa zargin ɗirkawa yarsa da ya haifa ciki, yar kimanin shekara 19."

Asali: Legit.ng

Online view pixel