Jam'iyyar APC Zata Lashe Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa, Kakakin Majalisa

Jam'iyyar APC Zata Lashe Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa, Kakakin Majalisa

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa babu tantama APC zata lashe zaɓukan kananan hukumomin jihar
  • A cewarsa waɗanda suke jagorantar PDP a baya sun sauya sheka zuwa APC, sabida haka APC zata samu nasara baki ɗaya
  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya yi kira ga mambobin APC su fara yakin neman zaɓe gida-gida domin jawo hankalin jama'a

Nasarawa - Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bayyana yaƙininsa cewa jam'iyyar APC zata lashe zaɓen kananan hukumomin jihar, wanda za'a gudanar ranar 6 ga watan Oktoba.

Abdullahi ya faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da yaƙin neman zaɓen APC a Toto, hedkwatar ƙaramar hukumar Toto, ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mutum 4 Sun Mutu, Yayin da Wata Motar Bas Dauke da Fasinjojin Jihar Kano Ta Zarce Kogi

Yace ƙaramar hukumar Toto na ɗaya daga cikin yankunan da APC take da karfi, ya kuma tabbatar da cewa APC ce zata lashe zaɓen ciyaman da na kansiloli.

Jihar Nasarawa
Jam'iyyar APC Zata Lashe Zaɓen Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa, Kakakin Majalisa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace:

"Babu wata jam'iyya kamar APC, karamar hukumar Toto zata cigaba da kasancewa tamkar gidan jam'iyyar APC."
"Masu rike da PDP a baya, yanzun sun dawo jam'iyyar APC. Saboda haka APC zata samu nasara a zaɓen 6 ga watan Oktoba."
"Ranka ya ɗaɗe, inason tabbatar maka da cewa ba zamu baka kunya ba a ƙaramar hukumar Toto, zamu samu nasara a zaɓe mai zuwa."

Ku shiga gida-gida neman ƙuri'u - Gwamna Sule

Gwamna Abdullahi Sule, ya roki masoyan jam'iyyar APC su fara yaƙin neman zaɓe gida-gida domin jawo hankalin mutane su zaɓi APC.

Sule, wanda mataimakinsa, Emmanuel Akabe, ya wakilta, ya yabawa kakakin majalisa da sauran jiga-jigan jam'iyya na yankin bisa sadaukarwarsu wajen goyon bayan APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

A wani labarin kuma Gwamnatin Zulum ta fara shiri na musamman kan mayakan Boko Haram da suka mika wuya

Gwamnatin jihar Borno ta kaddamar da fara shirin canza yan ƙungiyar Boko Haram da suka miƙa wuya, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan labaru, Abba Jato, yace ya zama wajibi a karbi masu mika wuyan domin mafi yawansu mata ne da ƙananan yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel