Gwamnatin Zulum ta fara shiri na musamman ga mayakan Boko Haram da suka mika wuya

Gwamnatin Zulum ta fara shiri na musamman ga mayakan Boko Haram da suka mika wuya

  • Gwamnatin jihar Borno ta kaddamar da fara shirin canza yan ƙungiyar Boko Haram da suka miƙa wuya
  • Kwamishinan labaru, Abba Jato, yace ya zama wajibi a karbi masu mika wuyan domin mafi yawansu mata ne da ƙananan yara
  • Gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin ne a fadar mai martaba shehun Borno, ranar Laraba a Maiduguri

Borno - Gwamnatin jihar Borno ta ƙaddamar da shirin sulhu da canza mayakan Boko Haram da suka miƙa wuya, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Shirin wanda ƙungiyar tarayyar turai, EU, ta ɗauki nauyi tare da taimakon kungiyar UNICEF, UND da kuma IMO.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da fara shirin a fadar mai martaba shehun Borno ranar Laraba a Maiduguri, Kwamishinan yaɗa labarai, Babakura Abba-Jato, yace akwai bukatar a amshi tubabbun yan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Kada ku tausayawa yan bindiga, ku buɗe musu wuta koda sun shiga cikin mutane, Gwamnan Arewa ya hasala

Yan Boko Haram da suka mika wuya
Gwamnatin Zulum ta fara shiri na musamman ga mayakan Boko Haram da suka mika wuya Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar kwamishinan cikinsu akwai mata da ƙananan yara, waɗanda yan ta'addan suka tilastawa zama a jeji, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan Boko Haram nawa suka mika wuya zuwa yanzu?

Abba Jato ya bayyana cewa mafi yawacin mutum 6,000 da suka miƙa wuya mata ne da yara kanana, sai kuma wasu mutane da yan ta'addan suka kwace yankunan su kuma suka tilasta musu zama suna musu noma.

Kwamishinan yace:

"Hakanan kuma akwai mayaƙan da suka ɗauki makami a baya cikin waɗanda suka mika wuya ga hukumomi."

Ya bayyana cewa a halin yanzu, ma'aikatar harkokin mata ita ke jagorantar shirin da ya ƙunshi mata da ƙananan yara.

Muna bukatar goyon bayan sarakunan gargajiya - UNICEF

A jawabinta, shugabar ofishin UNICEF a Maiduguri, Phuong Nguyen, ta jaddada bukatar goyon bayan iyayen ƙasa wato sarakunan gargajiya a wannan shirin.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari

"Mun zo nan ne (fadar shehun Borno) domin ƙara neman goyon bayanku yayin da gwamnatin jiha ta fara shirin canza ƙananan yara, waɗanda suke da alaƙa da ƙungiyar yan ta'adda."
"Ranka ya daɗe, waɗannan yaran mu ne, maƙotanmu, da kuma yan uwan mu maza da mata, waɗanda yan ta'adda suka kama lokaci daban-daban yayin rikici."
"Mafi yawancinsu sun rayu ne a wuraren da yan ta'adda suka kwace, suka maida su tamkar bayinsu, waɗanda suke musu hidima kala daban-daban."

Mutane sun kona gidan kwamishinan tsaro

A wani labarin na daban Bayan katse hanyoyin sadarwa, Fusatattun mutane sun kona gidan Kwamishinan Sokoto

Wasu fusatattun matasa sun kone gidan kwamishinan tsaro na jihar Sokoto, Garba Moyi, bisa ƙin halartar taron nemo hanyoyin magance matsalar tsaro.

Rashin zuwansa wurin taron ya fusata matasa, inda bayan ƙone gidansa, mutanen suka wuce gidan dagaci, suka farfasa masa mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: