Mutum 4 Sun Mutu, Yayin da Wata Motar Bas Ta Jihar Kano Ta Faɗa Kogi

Mutum 4 Sun Mutu, Yayin da Wata Motar Bas Ta Jihar Kano Ta Faɗa Kogi

  • Wata motar Bas da direbanta ya gaza sarrafata ta faɗa wani kogi, inda fasinjoji huɗu suka rasa rayuwarsu
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani yanki na jihar Kogi, kuma motar tana kan hanyarta na zuwa Kano
  • Kwamandan jami'an tsaron NSCDC na jihar, Suleiman Mafara, ya gargaɗi direbobin kan tukin gagganci

Kogi - Wata motar Bas mai ɗaukar mutum 18 ta faɗa kogi a Koton Karfe, jihar Kogi, inda mutum huɗu suka rasa rayuwarsu, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa motar ta yi hatsarin ne da misalin ƙarfe 7:30 na dare, ranar Talata da ta wuce.

Kwamandan hukumar kare haɗurra ta ƙasa (FRSC), Solomon Agure, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Motar bas ta faɗa Kogi
Mutum 4 Sun Mutu, Yayin da Wata Motar Bas Ta Jihar Kano Ta Faɗa Kogi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yace motar Bas ɗin mai lamabar rijista a jihar Filato, JJN 73 XA, ta taso ne daga Ijora ƙarƙashin gada a jihar Lagos kuma tana kan hanyar zuwa Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Agure yace mutum hudu daga cikin fasinjojin sun mutu, yayin da wasu guda bakwai suka ji munanan raunuka.

Rahotanni dun bayyana cewa direban motar ya kasa sarrafa motar ne yayin da lamarin ya faru saboda bacci ya kwashe shi.

Jami'an tsaro sun ceto wasu a raye

Kwamandan jami'an tsaro na NSCDC na jihar Kogi, Suleiman Mafara, yace bayan sun samu kiran gaggawa, jami'ansa da haɗin guiwar jami'an FRSC da yan sa kai sun kai agaji cikin sauri.

Yace:

"Jami'ai sun gano gawarwakin mutum huɗu yayin da suka ceto wasu mutum 13 a raye, sai kuma mutun ɗaya da ba'a gano ba."
"A halin yanzun jami'an mu sun bazama neman ragowar mutun ɗaya da ba'a gano ba, kuma an kai gawarwakin da aka gano ɗakin ajiye gawa."

Kwamanda ya gargaɗi direbobi su shiga taitayinsu

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

Kwamandan NSCDC ya gargaɗi direbobi da sauran matafiya da su kula da ƙa'idojin tuƙi domin gujewa faɗawa irin waɗannan hatsarin.

A wani labarin na daban kuma Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo/Karaye ta jihar Kano, Haruna Isah Dederi, yace saboda luguden wutan sojoji kan yan bindiga a Zamfara da Katsina, sun fara tserowa suna shiga jihar Kano.

A wani kudiri da ya gabatar a zaman majalisa na ranar Talata, yace a yan makonnin da suka gabata mahara sun kai hari wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Rogo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel