Arewa za ta cigaba da mulkar Nigeria ko wanene a kujerar shugaban ƙasa, Akintoye
- Farfesa Banji Akintoye, jigon yarabawa ya ce arewa ce za ta cigaba da mulki ko da dan kudu ne shugaban kasa
- Akintoye ya ce mutanen arewa sun dade suna juya kasar saboda yawansu kuma suna kokarin mamaye sauran yankunan
- Akintoye ya koka ne da hakan kwanaki kadan bayan Dr Hakeem Baba Ahmed na Dattawan Arewa ya ce babu wanda zai tilastawa arewa zaben wanda ba su so
Jamhuriyar Benin - Jagorar kungiyar Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye ya ce arewa ce za ta cigaba da mulkar Nigeria da mamaye ta koda kuwa wanene ke kan kujerar shugaban kasa.
Ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi daga Jamhuriyar Nijar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Akintoye ya yi wannan furucin ne kwanaki kadan bayan kungiyar dattawan arewa ta ce arewa ba za ta cigaba da sa ido ba a kasar duba da cewa ita ke da yawan al'umma.
Da ya ke jawabi a shirin na The Punch, Akintoye mai shekaru 86, Farfesan tarihi ya ce tun da dadewa arewa na son 'mamaye' dukkan kasar.
Duk da cewa bai fito fili ya yi nuni ga kalaman kungiyar na kakkakin dattawan arewa ba, Akintoye ya ce a yanzu Nigeria ba kasa bane domin kabilar daya na danne sauran.
Ya ce:
"A halin yanzu Nigeria ba kasa bace. Me yasa na ce hakan? Babu wata kasa a duniya da yanki daya za ta ce, 'za mu mamaye sauran, za mu mayar da su a karkashin mu, za mu rika juya albarkatun yankunan ku, za mu rika tafiyar da ku tamkar bayi."
Akintoye ya ce duk dacewa wasu yan kudu kamar tsohon shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan sun yi mulki bayan dawowar dimokradiyya, sun yi mulkin ne karkashin 'yan arewa.
A cewarsa:
"A karkashin mulkin Obasanjo, arewa ta sauya kundin tsarin mulkin kasa ta bawa jihohi damar kafa shari'ar musulunci. Obasanjo ya gaza yin komai a kai ... abu ne mai hatsari da aka kakabawa yan Nigeria kuma babu wanda ya iya komai a kai.
"Eh, Obasanjo dan mu ne, muna son shi amma mun san lokacin da ya yi mulkin kasa akwai wadanda ya ke yi wa biyayya a boye kuma babu wanda zai iya komai a kai. Ballanta mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
"Osinbajo mutum ne mai ilimi da basira, duba abin da ya ke yi, kana ganin da son ransa ya ke yi?."
APC ta gindaya wa FFK sharuddan da zai cika kafin ta gama amincewa da shi
A wani labarin daban, jam’iyya mai mulki a Najeriya, APC ta lissafo wa Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode tarin sharuddan da tace wajibi ne ya bi don ta amince da shi dari bisa dari.
Kamar yadda LIB ta ruwaito, darekta janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Dr Salihu Moh Lukman ya ce, wajibi ne FFK ya tafi wurin shugaban jam’iyyarsa na gunduma da kuma shugabannin APC na jiharsa ya yi rijista kuma ya amince tare da girmama ra’ayoyin duk wasu shugabanni da ‘yan jam’iyyar kafin ya zama cikakken dan jam’iyyar.
DG din PGF din ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba, inda ya ce mambobin jam’iyyar da dama sun hassala akan yadda shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya shirya wa FFK babbar liyafa a lokacin da ya bar PDP ya koma APC.
Asali: Legit.ng