Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

  • Jam'iyyar APC ta bayyana dalilin da yasa mambobinta ke kokawa da jin haushi kan komawar Kayode APC
  • Ya bayyana cewa, jam'iyyar ba yadda ta iya tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafe wa Kayode
  • Wannan na zuwa ne yayin da cece-kuce yayi yawa kan batun komawar Fani-Kayode zuwa jam'iyyar ta APC

Salihu Lukman, darakta janar na kungiyar gwamnonin ci gaba (PGF), ya bayyana dalilin da ya sa wasu mambobin jam’iyyar APC ke adawa da sauya shekar Femi Fani-Kayode zuwa cikinta.

A ranar Alhamis, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC sannan aka gabatar da shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja.

Sauya shekar tsohon ministan ya jawo cece-kuce mai zafi daga dubban 'yan Najeriya da dama, ciki har da mambobin APC, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jigon APC a Kano ya yi tir da tarbar da Buhari, APC suka yi wa Fani-Kayode a fadar Aso Villa

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A baya, Fani-Kayode ya soki manufofin APC, inda ya sha alwashin cewa ya gwammace ya mutu akan ya shiga jam’iyyar.

Da yake tsokaci game da batun, DG PGF, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi 19 ga watan Satumba, ya ce mambobin APC sun yi mamakin babban liyafar da aka shirya wa Fani-Kayode, wanda ya ce yana da “dabi’ar maciji”.

Lukman, duk da haka, ya shawarci membobin APC da su fahimta, ya kara da cewa ya kamata a yarda da shawarar shugabancin jam’iyyar.

Ya kamata mambobin APC su fahimta, kuma Buhari ya yafewa Kayode

A bangare guda, DG PGF ya bayyana cewa, duk da ana jin haushin zuwan Kayode APC, amma ya kamata mambobin jam'iyyar su fahimta, kana shugaba Buhari ya riga ya yafewa Kayode.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Pulse ta ruwaito Salihu Lukman na cewa:

"Zanga-zangar adawa da shigar Fani-Kayode APC tana da nasaba da dabi'ar sa, yana cin zarafi, cin mutunci, da tozarta kowa, kusan ba tare da nuna bambanci ba."
“Kusan kowane dan APC yana jin haushin cewa shugabannin mu sun kawo wani kamar Fani-Kayode cikin jam’iyyar mu. Wannan ya yi muni ta hanyar shirya masa liyafa, wanda bai cancanta ba.
“Amma tunda abin ya faru, babu bukatar kuka kan madarar da ta zube. Abin da ya fito karara shi ne, shugabanninmu, musamman Shugaba Buhari sun yafe wa Fani-Kayode kuma sun rungume shi a matsayin daya daga cikin mu.
“Sabanin haka, wadanda ke da aminci da biyayya ga jam’iyyarmu da shugabanninmu da kyar suka sami girman da ya kamata su samu.

Ya kuma yi kira da mambobin APC da su karbi Kayode hannu bibbiyu kana su girmama shi a matsayinsa na mamba a jam'iyyar.

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu karbuwa a jam'iyyun siyasa 17 na kudunci

Kara karanta wannan

Ina gidan Farfesa Pantami jiya har cikin dare, mun debi girki kuma mun tattauna: Femi Fani-Kayode

A wani labarin, shugabannin jam’iyyun siyasa 17 da kungiyoyin farar hula a jihar Delta a ranar Lahadin da ta gabata sun amince da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Amincewar tana zuwa ne bayan bukatar gwamnoni jihohi 17 na kudancin kasar na neman shugaban kasa daga kudanci, Punch ta ruwaito.

Gamayyar kungiyar Atiku Support Groups Initiative wacce ta sanar da amincewar ta yi ikirarin cewa bai kamata kabilanci ko bambancin siyasa su zama abin duba ga tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel