Gwamna Ganduje, yan majalisar wakilan Kano sun dira Landan don gaida Tinubu

Gwamna Ganduje, yan majalisar wakilan Kano sun dira Landan don gaida Tinubu

  • Bayan walimar kammala karatun 'dansa, Ganduje ya leka wajen Bola Tinubu
  • Asiwaju Tinubu ya dade yana jinya bayan yi masa tiyata a Landan
  • Ganduje ya samu rakiyar 'dansa tare da yan majalisar Kano

Landan - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya shiga jerin manyan jiga-jigan siyasan da suka garzaya birnin Landan domin gaida jagoran jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

A watan Yuli ne jita-jita suka yi ta yawo cewa an kwantar da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, a wani asibitin waje, za ayi masa aiki.

Mai magana da yawun bakin babban ‘dan siyasar, Tunde Rahman, ya kartaya wannan batu, yace Tinubu ya na kasar waje, amma ba jinya yake yi ba.

Ganduje tare da 'dansa, Muhammad Umar, da kuma wasu yan majalisar dokokin jihar Kano suka kaiwa jagoran siyasan ziyara.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy

Legit Hausa ta ci karo da hotunan ziyarar da wani Abubakar Aminu Ibrahim ya daura a shafin Facebook.

Gwamna Ganduje, yan majalisar wakilan Kano sun dira Landan don gaida Tinubu
Hoto: Abubakar Aminu
Gwamna Ganduje, yan majalisar wakilan Kano sun dira Landan don gaida Tinubu
Asali: Facebook

Ana ta kai wa Tinubu ziyara Landan

A makon da ya gabata Sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun tafi birnin Landan, kasar Ingila domin gaishe da Bola Tinubu.

Daga cikin Sanatocin akwai Sanata Olamilekan Solomon mai wakiltar Legas ta yamma; Sanata Tokunbo Abiru mai wakiltan Legas ta gabas da kuma Sanata Opeyemi Bamidele mai wakiltan Ekiti ta tsakiya.

Sauran sune Sanata Adeyemi Oriolowa mai wakiltar Osun da Sanata Sani Musa na jihar Neja.

Gabanin tafiyarsu, Abdulaziz Yari da Sanatan Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko sune ‘yan siyasan yankin Arewa na farko da suka ziyarci Tinubu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun damke Miji da Mata sun sace sabon 'dan jariri

Suma kafinsu tsohon gwamnan Ogun, Sanata Ibikunle Amosun da Sanata Tokunbo Afikuyomi sun kai ziyarar.

Sannan Gwamnonin Ondo da Ekiti, Rotimi Akeredolu da Dr. Kayode Fayemi suka kai tasu ziyarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel