Manyan ‘Yan siyasan Arewa sun kai wa Tinubu ziyara taka-nas a Landan, sun kashe hotuna

Manyan ‘Yan siyasan Arewa sun kai wa Tinubu ziyara taka-nas a Landan, sun kashe hotuna

  • Abdulaziz Yari da Aliyu Magatakarda Wamakko sun kai wa Bola Tinubu ziyara
  • Wannan ne karon farko da ‘yan siyasa daga Arewa suka ziyarci Tinubu a waje
  • Tinubu bai rike da sanda yayin da ya dauki hoto tare da Yari, Sanata Wammako

London - ‘Yan siyasan Najeriya suna cigaba da zuwa kai wa tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu ziyara yayin da yake kasar Birtaniya.

Wannan karo, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko suka ziyarci Bola Tinubu.

PM News tace tsofaffin gwamnonin sun gana da babban ‘dan siyasar, kuma daya daga cikin jiga-jigan APC a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, 2021.

Abdulaziz Yari da Sanatan Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko sune ‘yan siyasan yankin Arewa na farko da suka ziyarci Tinubu a fili.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Kafin zuwansu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka da kansa zuwa gidan Asiwaju Bola Tinubu lokacin da ya ziyarci likitocinsa kwanan baya.

Bola Tinubu in London
Abdulaziz Yari da Aliyu Wamakko a gidan Bola Tinubu Hoto: BBC News Yoruba Daga; Facebook
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abdulaziz Yari yana cikin wadanda ke neman kujerar shugaban jam’iyyar APC. Shi kuma Magatakarda Wamakko jagoran APC ne a jihar Sokoto.

Legit.ng tace ana tunani an yi wa Tinubu aiki a gwiwa, sai ya tsaya domin ya murmure. A jiya an ga hoton shi ba tare da sanda ba, alamun ya samu sauki.

An kai wa Tinubu ziyara kwanaki

A makon da ya gabata, wadanda suka ziyarci Bola Tinubu sun hada da tsohon gwamnan Ogun, Sanata Ibikunle Amosun da Sanata Tokunbo Afikuyomi.

Sannan Gwamnonin Ondo da Ekiti, Rotimi Akeredolu da Dr. Kayode Fayemi sun ziyarci jagoransu.

Kafin nan Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya hadu da uban gidan na sa kuma tsohon gwamnan Legas bayan ya shafe sama da wata daya a kasar wajen.

Kara karanta wannan

Allah zai bamu shugaba kamar Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

Meya ke damun Tinubu

A watan Yuli ne jita-jita suka yi ta yawo cewa an kwantar da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, a wani asibitin waje, za ayi masa aiki.

Mai ba magana da yawun bakin babban ‘dan siyasar, Tunde Rahman, ya kartaya wannan batu, yace Tinubu ya na kasar waje, amma ba jinya yake yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel