Yan sanda sun damke Miji da Mata sun sace sabon 'dan jariri

Yan sanda sun damke Miji da Mata sun sace sabon 'dan jariri

  • Barayin Jariri sun shigo hannun jami'an yan sanda a jihar Kano
  • Miji da matan sun sace jaririn ne a asibitin Muhammad Abdullahi Wase, Kano
  • Tuni an gano jaririn kuma an mayar da shi wajen iyayensa na kwarai

Kano - Hukumar yan sanda a jihar Kano ranar Juma'a ta damke wata Mata da Mijinta da suka sace sabon jaririn wani mutumi da matarsa ta haifa masa 'yan biyu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a jawabin da ya saki ya bayyana sunan Mijin matsayin Abubakar Sadiq da matarsa Maryam Sadiq, rahoton PRNIgeria.

A cewarsa, Maryam ta bayyana cewa ta sace jaririn ne saboda Mijinta ya dade yana neman 'da na miji.

Kakakin yan sandan ya kara da cewa Abubakar da matarsa Maryam da wuri suka shirya Walima a gidansu dake Rijiyar Zaki Quarters, Kano da sunan cewa sun samu karuwa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Hakan ya sa mutane suka fara zargi saboda "makwabta sun ce Maryam ba tada juna biyu."

A daidai ranar kuwa, DSP Kiyawa yace wani mutumi mai suna Rabiu Muhammad ya kai karar cewa an sace masa sabon jariri cikin 'yan biyun da matarsa ta haifa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace Surukarsa dake lura da yaran ta buge da bacci ne kawai ta farka babu yaro guda.

Yan sanda sun damke Miji da Mata sun sace sabon 'dan jariri
Yan sanda sun damke Miji da Mata sun sace sabon 'dan jariri Hoto: PRNigeria
Asali: Facebook

Yace:

"Matar Muhammad ya haifi yan biyu ranar 07/09/2021 a asibitin koyarwan Muhammad Abdullahi Wase, Kano."
"Ba tare da bata lokaci ba, hukumar ta kaddamar da bincike. An kulle asibitin kuma aka gudanar da bincike amma ba a ga yaron ba."
"Daga bayan aka gano Maryam Sadiq da Abubakar, yan Rijiyar Zaki Quarters, Kano. An kwato yaran daga hannunsu."

Ya kara da cewa tuni an mayar da yaron wajen iyayensa na gaske.

Asali: Legit.ng

Online view pixel