Da duminsa: An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy

Da duminsa: An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy

  • Bayan mutuwar Abubakar Shekau, wani babban shugaban yan ta'adda ya mutu
  • Mus'ab Albarnawy ne wanda ya kashe Abubakar Shekau kwanakin baya
  • Albarnawy shine 'dan wanda ya kafa kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf

Bayan shekaru da dama ana farautarsa, an samu nasarar hallaka shugaban yan ta'addan ISWAP Mus'ab Albarnawy a jihar Borno, rahoton DailyTrust.

An samu rahoton cewa an kashe Albarnawy ne a karshen watan Agustan 2021.

Mus'ab Al-Barnawi ne 'dan mu'asassin Boko Haram, Mohammed Yusuf, wanda shine jami'an tsaro suka kashe a 2009 yayinda yayi fito-na-fito da gwamnati.

A shekarar 2016, kungiyar ISIS ta alanta Albarnawy a matsayin shugabanta na yankin Afrika ta yamma.

Da duminsa: An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy
Da duminsa: An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Hotunan Ganduje da Goggo a London yayin da ɗansu ya kammala digiri

Ta yaya aka kashe Al-Barnawi?

An samu riwayoyi biyu game da labarin mutuwarsa. Yayinda riwayar farko tace Sojojin Najeriya ne suka hallakashi, wata riwayar tace rikicin cikin gida tsakaninsa da sauran yan ta'addan ISWAP yayi sanadiyar mutuwarsa.

Riwayar farko ta dogara ne kan maganganun wasu jami'an tsaron dake faggen fama inda sukayi ikirarin cewa an hallakashi ne tare da wasu kwamandojin ISWAP kimanin biyar.

Wata majiya ta bayyana cewa an kasheshi a Bula Yobe, wani gari dake iyakan jihar Yobe da Borno.

Amma wata majiyar daban ta ce ya mutu ne a Yale, Bama.

Daily Trust tace ta samu labari daga wasu majiyoyi cewa rikicin shugabanci yayi sanadiyar mutuwar Albarnawy.

An samu labarin cewa tsakanin 14 ga Agusta an 26 ga Augustan 2021, sun yi rikici tsakaninsu kuma an yi rashin kwamandoji da dama.

Hakazalika wata majiyar ta ce dayar bangaren ta dauko hayan Sojoji daga tsakiyar Afrika domin yiwa Albarnawy juyin mulki kuma sun samu nasara.

Kara karanta wannan

Ku taimakawa Almajirai wajen samun ilmin Boko: Rochas Okorocha

Har yanzu dai hukumar Sojojin Najeriya bata tabbatar ko karyata rahoton kisan Albarnawy ba.

Hakan bai rasa alaka da cewa a al'adar hukumar, bata fiya sanarwa kan mutuwar wani babban dan Boko Haram idan ya kasance ba jami'anta suka hallakashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel