Da duminsa: Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn

Da duminsa: Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn

  • Majalisar jihar Kano ta lamunce wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kudirinsa na karbo bashin N4bn
  • Kamar yadda takardar da gwamnan ya mika gaban 'yan majalisar ta ce, za a yi amfani da bashin ne wurin aikin wutar Tiga da Challawa
  • Kakakin majalisar, Ibrahim Chidari ya karanta wasikar ga majalisar yayin da Uba Abdullahi ya bukaci 'yan majalisar da su amince

Kano - Majalisar jihar Kano ta amince wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya karbo bashin N4 biliyan da ya ke nema domin kammala ayyukan wutar lantarki na Tiga da Challawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an amince da karbo bashin ne yayin zaman majalisar wanda ya samu shugabancin kakakin majalisar jihar Kano, Ibrahim Chidari.

Da duminsa: Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn
Da duminsa: Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn. Hoto daga www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a wata takarda da aka mika wa daraktan yada labarai na majalisar, Uba Abdullahi, wanda ya ce majalisar ta zauna kan al'amarin bayan kakakin ya karantowa majalisar da gwamnan ya tura musu.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisa ya musanta kwatanta IPOB, 'yan Yarbawa da Boko Haram

Kamar yadda yace, shugaban masu rinjaye na majalisar yayi kira ga majalisar da su duba bukatar domin ba da damar karbo bashin, wanda ya ce zai matukar amfanar jihar, Daily Trust ta ruwaito.

"Bayan tattaunawa da majalisar ta yi, ta amince da bukatar gwamnan na neman bashin," yace a takardar.

Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa

A wani labari na daban, wata kotun shari'a da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, a ranar Laraba ta umarci wani malamin makaranta, Yusuf Yusuf da ya datse dukkan wata soyayya da ke tsakaninsa da dalibarsa mai suna Zainab Muhammad.

Alkali Murtala Nasir, ya umarci malamin da ya biya N8, 500 ga Zainab a matsayin kudin shigar da kara da kuma kudin asibiti da ta biya bayan mugun dukan da yayi mata.

Kara karanta wannan

Barin wuta ta sama: Gwamnan Yobe ya umurci asibitocin gwamnati da su kula da wadanda suka jikkata

Alkalin ya yanke wannan hukuncin bayan sasancin da su biyun suka yi ba a kotu ba, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng