'Yan ta'adda da 'yan bindiga sun mamaye murabba'in mita 1,129 na gandun dajin Najeriya
- An ruwaito daga majiya cewa, dazuka a Najeriya na dankare da 'yan ta'adda da 'yan bindiga
- Rahoto ya ce, 'yan ta'adda sun mamaye akalla murabbi'in mita 1,129 na dazukan Najeriya
- A cewar hukumomi, wannan babban kalubale ne ga tsaron kasar, kuma akwai bukatar neman mafita
Ibrahim Musa Goni, babban jami'i kuma masanin kula da gandun daji a hukumar NPS, ya ce 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya sun mamaye murabba'in 1,129 na gandun dajin kasar, TheCable ta ruwaito.
Da yake magana lokacin da ya ziyarci Lucky Irabor, babban hafsan tsaro (CDS), a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata 14 ga watan Satumba, Goni ya ce tawagarsa a shirye take ta hada gwiwa da sojoji wajen kawar da 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya.
Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi
Goni ya ce an kafa ayyukan gandun daji ne don karewa da kuma kare rayayyun halittu a yankunan da aka sani da wuraren shakatawa na kasa, wuraren adana namun daji da kuma gandun daji.
Benjamin Sawyerr, daraktan watsa labarai na Hedkwatar Tsaro, ya nakalto yana fadi a cikin wata sanarwa cewa:
"Wadannan wuraren ajiyar gandun daji da wuraren shakatawa na kasa wadanda ke da murabba'in 1,129 sun zama maboyar 'yan bindiga da' yan ta'adda."
Goni ya ce akwai bukatar aikin soji da na jami'an shakatawa na ci gaba da aiki tare don magance kalubalen tsaro na kasar.
A cewarsa:
"Sojojin na iya taimakawa wajen aikin shakatawa ta hanyar horas da ma'aikatan ta kan tsaron gandun daji."
Meye martanin soji kan wannan batu?
A nasa bangaren, Irabor, wanda Dahiru Sanda, mataimakiyar madugun jiragen sama ya wakilta, ya ce sojoji sun dukufa wajen tabbatar da cewa kasar nan ta zauna lafiya.
Shugaban tsaron ya ce dole ne masu ruwa da tsaki da suka dace su tallafa wa aikin gandun daji don tabbatar da cewa an kare dazuka daga masu laifi.
Irabor ya nemi ma'aikatar shakatawa ta Goni da ta ba da bayanan sirri ga sojoji da za su taimaka wajen yakar masu laifi.
Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce hauhawar rashin aikin yi na kawo hadari ga Najeriya, Punch ta ruwaito.
Ya danganta rashin ilimi ga matsalolin da ke addabar kasar, yana mai gargadin cewa idan ba a yi maganin lamarin ba, kasar za ta iya “shafewa gaba daya.”
Ministan ya fadi haka ne a taron koli na tattalin arzikin hadin gwiwa da ma'aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci suka shirya a Abuja ranar Talata 14 ga watan Satumba.
An yiwa taron take da, 'Fassara Manufofin Ci Gaba mai Dorewa zuwa kasuwancin cikin gida a Najeriya.'
Ngige ya ce:
“Muna cikin matsala a matsayin kasa. Muna cikin matsala kuma duk wanda ya gaya muku bai san muna cikin matsala ba yana yi wa kansa karya ne kuma ya muku karya.
Akidar Boko Haram yaudara ce tsagwaronta
A wani labarin daban, Wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar 'yan ta’addan Boko Haram zamba ce.
A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta'addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su.
A cewar Mista Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa iya tunkarar sojoji sai dai buya daga baya suna amfani da mayakansu wajen kai hare-haren kan sojoji a arewa maso gabas.
Asali: Legit.ng