An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

  • Wani ikirari daga Lauretta Onochie na nuni da cewa an cafke wani babban kwamanda a kungiyar IPOB/ESN
  • A cewar hadimar shugaban kasar, dan ta’addan da ake zargi ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin
  • Matashin ya ce ana zargin cewa shugaban wata karamar hukuma a jihar kudu maso gabas shi ne mai kashewa kungiyoyin kudi

Hadimar shugaban kasa ta fuskar yada labarai, Lauretta Onochie, a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, ta sanar da cewa jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) sun cafke wani da ake zargin kwamandan IPOB / ESN ne.

A shafinta na Facebook, Onochie ta bayyana cewa mai laifin da aka kama ana masa laƙabi da Shakiti Bobo.

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin
'Yan sanda sun kama kwamandan IPOB / ESN Shakiti-Bobo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cikin bidiyon, wanda ake zargin wanda ba a bayyana sunansa na ainihi ba ya ce wani shugaban karamar hukuma a jihar kudu maso gabas ne ke daukar nauyin kungiyar.

Kara karanta wannan

Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton

Matashin saurayin da ke daure da ankwa ya yi wa jami'an tsaro alkawarin zai nuna musu bidiyon da zai tabbatar da ikirarin nasa.

Sai dai Legit.ng ba ta iya tabbatar da sahihancin bidiyon da hadimar shugaban kasar ta wallafa ba a lokacin rubuta wannan rahoton.

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

A wani labarin, mun ji a baya cewa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi zargin cewa haramtaciyyar kungiyar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB) na samun goyon bayan wasu ‘yan kasashen waje da ake biyansu albashi mai tsoka.

Buhari ya yi wannan zargin ne a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okonjo-Iweala, Peter Obi da wasu 'yan siyasa 16 na kudu maso gabas da aka nemi suyi takara

Ya yi zargin cewa kungiyar tana aikata ayyukan ta’addanci ne domin satar kudi. Buhari ya bayyana cewa IPOB ba gwagwarmayar neman 'yanci take yi ba yayin da suke kai hari kan ofisoshin 'yan sanda da kadarori.

Asali: Legit.ng

Online view pixel