Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

  • Jagororin APC na Taraba suna sha’awar rike mukamin Ministan wuta
  • Shugaban jam’iyyar na Taraba yace mutane har 32 suke harin kujerar
  • Daga ciki akwai Garba Umar, Sani Danladi da Sanata Yusuf Abubakar

Taraba - Akalla jagororin jam’iyyar APC 32 a jihar Taraba suna neman maye gurbin Saleh Mamman, wanda aka tsige daga mukamin Ministan wuta.

Jaridar Daily Trust tace manyan ‘yan siyasan Kano da Taraba inda Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman suka fito, suna hangen kujerun Ministocin tarayya.

Ana sa rai shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tura sunayen wadanda za su maye guraben Ministocin da ya kora da zarar ‘yan majalisa sun dawo aiki.

Shugaban APC na Taraba, Barista Ibrahim El-Sudi yace ‘ya ‘yan jam’iyyar 32 suke son wannan kujera.

Su wanene ke neman Minista?

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake kashe mutane 12, sun raunata wasu Bayin Allah a Kaduna

El-Sudi bai ambaci sunayen masu sha’awar kujerar ba, yace babu wanda ya tuntubi jam’iyyar domin kamun kafa, amma yace ya kamata a bar ta a jihar.

Wadanda ake gani sun kwallafa ransu wajen zama Minista a gwamnatin Buhari sun kunshi tsofaffin gwamnoni, Sanata, Jakadu da kuma kwamishinoni.

Taron FEC
Shugaban kasa a taron FEC Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

Tsofaffin gwamnonin rikon kwarya da aka yi a jihar; Alhaji Garba Umar da Sani Danladi Abubakar suna cikin wadanda suke sa ran samun mukamin.

Haka zalika akwai Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, tsohon Jakadan Najeriya zuwa kasar Trinidad and Tobago, Alhaji Hassan Jika Ardo da kuma Cif David Kente.

Rahoton yace shi ma tsohon kwamishinan tattali na jihar Taraba, Alhaji Ahmed Yusuf, yana neman kujerar. Yusuf ya taba neman takarar gwamna a baya.

Wasu masu neman zama Ministocin sun tattara sun koma birnin tarayya Abuja, sun tafi fadar shugaban kasa domin su nemi alfarmar masu madafan iko.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hon. Elumelu ya bayyana Gwamnan da zai iya hambarar da APC daga kan mulki

Gwamnan Delta ya nemi shugaban kasa

Shugaban marasa rinjaye a majalisar tarayya, Ndudi Elumelu ya lallabi Gwamnan Delta, Sanata Ifeanyi Okowa ya fito neman kujerar Shugaban kasa a 2023.

Hon. Ndudi Elumelu ya kamata Gwamna Okowa ya nemi mulki a PDP domin a kifar da APC a zabe mai zuwa na 22023, a cewarsa APC ta kashe Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel