Shugabannin Boko Haram matsorata ne: Tubabben kwamandansu ya tona asiri

Shugabannin Boko Haram matsorata ne: Tubabben kwamandansu ya tona asiri

  • Wani kwamandan Boko Haram ya bayyana illolin da ya fuskanta lokacin da yake dajin Sambisa
  • Ya bayyana cewa, kungiyar Boko Haram ba komai bane face zamba, kuma ana amfani da su ne a kashe su
  • Ya ce, shugabannin Boko Haram matsorata ne ba sa shiga fagen daga a gwabza yaki dasu ko sau daya

Wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar 'yan ta’addan Boko Haram zamba ce.

A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta'addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa

A cewar Mista Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa iya tunkarar sojoji sai dai buya daga baya suna amfani da mayakansu wajen kai hare-haren kan sojoji a arewa maso gabas.

Shugabannin Boko Haram matsorata ne: Tubabben kwamandansu ya tona asiri
Tubabben kwamandan Boko Haram | Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Mista Rugurugu ya kuma yi wa sojojin Najeriya addu'ar nasara, tare da hada wa da la'antar wadanda ba sa son zaman lafiya a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“… Sojojin da ke tausaya mana ba tare da cin zarafi ko musguna mana ba, muna addu’ar Allah ya kara musu daraja. Duk wanda zai kawo tashin hankali a Najeriya da kuma wanda baya son zaman lafiya ya wanzu, Allah ya nisanta shi da mu gaba daya."

Ya kuma shawarci sauran 'yan Boko Haram da ke daji da cewa, su mika kansu ga sojoji zai fi musu alheri, inda yake cewa:

"Ni da kaina, ga 'yan uwana da har yanzu suke cikin daji, mun zabi mu aje makamai mu kuma mika kanmu don samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

"Ya kamata ku zama masu rikon amana, kowa zai yaba muku kuma gwamnati tana cika alkawuran da ta dauka, suna kula kan komai, duk wanda bai tuba ya gyara halayensa ba, tabbas za a dauki mataki a kansa."

A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG

Tsohon shugaban horaswa da ayyuka a Hedikwatar rundunar Soji da ke Abuja, Birgediya Janar John Sura (mai ritaya), a ranar Juma'a, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tura 'yan ta'addan Boko Haram sama da 1,000 da suka tuba zuwa gona.

A cewarsa, ya kamata a yi amfani da su wajen aikin gona da suka hana ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya yi.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken 'Ku dauki 'yan ta'addan Boko Haram da suka tuba a matsayin fursunonin yaki', jaridar Punch ta ruwaito.

Sura, wanda ya bayyana 'yan ta'addan da suka tuba a matsayin fursunonin yaki, ya bayar da hujjar cewa ya kamata a yi gyara ga Yarjejeniyar Geneva wacce ta ba su wasu gata kamar kariya daga duk wani aiki na tashin hankali gami da tsoratarwa, cin mutunci da sauransu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga za su yi mubaya’a idan har aka zaɓi shugaban ƙasa mace a Nigeria, Lauya

Ya jaddada cewa ya kamata a kula da su a matsayin mutanen da ke zaman gidan yari kuma a sanya su cikin yanayin da ke ƙasa da na ‘yan sansanin gudun hijira.

Ya ce:

"Game da 'yan Boko Haram da suka tuba, ya kamata a kula da su a matsayin mutanen da ke cikin kurkuku tare da aiki mai tsanani.

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

A wani labarin, Kwamandan makarantar tsaro ta sojoji wato NDA, Ibrahim Yusuf, ya yi wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai bayani game da harin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai makarantar.

A yayin harin a ranar 24 ga watan Agusta, an kashe jami’an soji guda biyu sannan an yi garkuwa da daya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ba da rahoton cewa kwamandan ya gana da kwamitin ne cikin sirri, kamar yadda kwamandan ya ce an tsara takardun da za a gabatar wa membobin kwamitin.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Mista Yusuf kafin taron ya shiga ganawar sirri, ya ce zai yiwa kwamitin bayani kan kokarin da sojoji ke yi na kubutar da jami'in da aka sace.

Ya bayyana cewa Babban Hafsan Tsaro, Lucky Irabor, ya ziyarci inda aka kai harin a ranar da abin ya faru, ya kara da cewa wasu manyan sojoji da ke aiki da wadanda suka yi ritaya su ma sun ziyarci wajen.

Don haka Shugaban Kwamitin, Babajimi Benson (APC-Lagos), ya nemi 'yan jarida da ke wurin da su fice, amma ya ce kwamitin zai bincika kan kokarin da ake yi na ceto jami'in da aka sace

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel