Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu daga lissafin 2023

Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu daga lissafin 2023

  • Alex Kadiri yace duk Arewa maso tsakiya babu wanda zai iya rike Najeriya
  • Tsohon Sanatan na ganin Rotimi Amaechi ya dace da zama shugaban kasa
  • Sanata Kadiri ba ya goyon mulki ya koma hannun Bola Tinubu a zaben 2023

Kogi - Daya daga cikin manyan jam’iyyar APC, Sanata Alex Kadiri ya yi kira ga ‘yan siyasar Arewa maso tsakiya su hakura da yin takarar shugaban kasa.

Punch ta kawo rahoto cewa Alex Kadiri ya ba ‘yan siyasar da suka fito daga wannan yanki shawarar su nemi kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Tsohon ‘dan majalisar na Kogi ta gabas ya bada wannan shawara ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a Abuja a ranar 8 ga watan Satumba, 2021.

'Yan Arewa maso gabas ba za su iya ba

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Basarake Ya Zage Yana Yi wa Bola Tinubu da Gwamnan APC Kamfe

“Ina cikin jagororin Arewa maso tsakiya, suna kira na wajen duk wani taronsu. Babu wani daga Arewa maso tsakiya da zai iya zama shugaban kasa a 2023.”
“Ku nuna mani wanda zai iya, ku kawo shi. A shekaruna, babu abin da nake nema daga wurin wani. Ba komai nake nema ba, ra’ayina ne kurum nake fada.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga-jigan APC
APC ta na kamfe a Kogi Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Menene matsayin Arewa, Ibo da Yarbawa a 2023?

Kadiri yana so ‘Yan Kudu su fito da shugaba a 2023, amma tun da Olusegun Obasanjo da Yemi Osinbajo sun shiga Aso Rock, ya kamata Yarbawa su hakura.

The News ta kawo wannan rahoto, tace ‘dan siyasar yana da ra’ayin cewa ‘yan Arewa maso yamma su yafe mulki tun da dai Muhammadu Buhari ya yi.

“Ibo surukai na ne, bani da kulli game da su. Maganar gaskiya ita ce wannan halin da suke da shi, ba zai bari su karbi mulkin Najeriya a yanzu ba (2023).”

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

“Ko kun ki, ko kunso, Rotimi Amaechi ya cancanta. Ya san aiki, kuma yana da lafiya. Ba zai yiwu daga ‘Yaradua da Buhari, mu koma wa Bola Tinubu ba.”
“Idan Rotimi Amaechi da gwamna Babagana Zulum za su iya hada-kai, kasar nan za ta yi kyau.”

PDP ta yi damarar kifar da APC

A yau ne mu ka ji cewa Gwamnonin adawa za su sake zama na musamman domin su shirya wa taron NEC, sannan a kawo karshen tirka-tirkar da PDP ta shiga.

Rahotanni sun ce shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya kira zama a yau domin su fara yin tanadin zaman NEC da zaben shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel