A ƙarshe, APC ta yi magana kan raɗe-raɗin Goodluck Jonathan zai shigo jam'iyyar

A ƙarshe, APC ta yi magana kan raɗe-raɗin Goodluck Jonathan zai shigo jam'iyyar

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta ce tana maraba da Goodluck Jonathan idan zai shigo jam'iyyar
  • Sanata John Akpanudoedehe, sakataren APC na kasa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba
  • Sai dai a bangarenta, jam'iyyar adawa ta PDP ta ce wannan kawai shaci-fadi ne mafarki da wasu ke yi

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a ranar Laraba ta ce za ta karbi tsohon shugaban kasar Nigeria, Goodluck Jonathan idan yana da sha'awar shigowa jam'iyyar, The Punch ta ruwaito.

Ta kuma ce zai kuma mora duk wani alfarma da gata kowanne dan jam'iyyar ke da shi ba tare da la'akari da lokacin da ya shigo jam'iyyar ba.

Muna maraba da Goodluck Jonathan idan zai dawo jam'iyyar mu, APC
Shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Magantu Kan Raɗe-Raɗin Shigarsa Jam’iyyar APC

A cewar rahoton na The Punch Sakataren jam'iyyar na kasa, Sanata John Akpanudoedehe ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi a shirin Channels Television mai suna Politics Today.

Da ya ke amsa tambayar da aka masa kan rade-raden cewa jam'iyyar na zawarcin Jonathan domin ya tsaya mata takarar shugaban kasa a 2023, ya ce:

"Bana son yin magana mara tabbas."

Ya cigaba da cewa:

"Kowa ya iya shiga APC, muna maraba da duk wanda ke son shiga. Muna kara karfi kan shirin da muka saka a gaba. Yau na fara jin wannan labarin, idan ya zo, za mu karbe shi, hakan zai iya zama labari mai kyau."
"A taron da kwamitin shugabanni suka yi na karshe sun ce kowa na iya shigowa jam'iyyar ya kuma nemi takarar duk wata kujera da ya ke so."

Akpanudoedehe ya ce yana tsamanin wasu karin gwamnonin PDP za su shigo jam'iyyar na APC kafin watan Disamba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

Abin da kakakin PDP na kasa ya ce game da batun?

Da aka tuntube shi domin ji ta bakinsa, mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya ce:

"Jita-jitar cewa tsohon shugaban kasar mu da wasu gwamnonin mu za su koma jam'iyyar APC, labarin kanzon kurege ne, mafarki ne kawai da wasu ke yi kuma babu kanshin gaskiya a batun."

Asali: Legit.ng

Online view pixel